A karon farko, ministan Buhari ya harbu da cutar COVID-19

A karon farko, ministan Buhari ya harbu da cutar COVID-19

- Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya harbu da cutar COVID-19

- Onyeama da kansa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli

- Ya tabbatar da cewar yana kan hanyarsa ta zuwa cibiyar killacewa

Geoffrey Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya, ya kamu da cutar korona.

Onyeama ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli, cewa yana kan hanyarsa ta zuwa cibiyar killacewa.

"Na yi gwajin cutar korona karo na hudu a jiya bayan alamun ciwon makogwaro, sai dai kuma abun bakin ciki shine ya bayyana ina dauke da cutar a wannan karon.

"Wannan ita ce rayuwa, ka yi nasara a nan, ka fadi a can. Ina hanyar zuwa cibiyar killacewa kuma ina addu'ar dacewa da mafificin alkhairi," ya wallafa.

Onyeama ne minista na farko da ya kamu da muguwar cutar a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Dakarun sojin Najeriya sun halaka manyan kwamandoji

A gefe guda, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 653 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:25 na daren ranar Asabar 18 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 653 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-115

Kwara-85

Enugu-80

FCT-78

Rivers-36

Ondo-35

Oyo-30

Katsina-28

Kaduna-19

Abia-19

Nasarawa-18

Plateau-17

Imo-16

Ogun-9

Ebonyi-9

Benue-9

Kano-9

Delta-8

Bauchi-7

Ekiti-6

Gombe-4

Bayelsa-4

Adamawa-4

Osun-4

Cross River-1

Yobe-1

Borno-1

Zamfara-1

Har ila yau ga alamomin cutar Korona da ya kamata ka sani:

1. Tari da lamin baki ko gujewar jin kamshi ko wari

2. Tari da wahalan numfashi

3. Tari da gudawa

4. Tari da mura

5. Tari da kasalar jiki

6. Tari da rawan jiki 7. Tari da ciwon jiki 8. Tari da ciwon kai 9. Tari da ciwon makogwaro

10. Zazzabi da lamin baki ko gujewar jin kamshi ko wari 11. Zazzabi da wahalan numfashi 12. Zazzabi da gudawa

13. Zazzabi da mura

14. Zazzabi da kasalar jiki

15. Zazzabi da rawan jiki

16. Zazzabi da ciwon jiki

17. Zazzabi da ciwon kai

18. Zazzabi da ciwon makogwaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng