Tsohon bulaliyar majalisar dattawa, ya koma jam'iyyar PDP

Tsohon bulaliyar majalisar dattawa, ya koma jam'iyyar PDP

- Tsohon bulaliyar majalisar dattawa, Roland Owie, a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, ya sauya sheka daga jam'iyyar ADP zuwa jam'iyyar PDP

- Owie ya yi kira ga magoya bayansa da su dage wajen tabbatar da komawar Gwamna Godwin Obaseki kujerarsa

- Ya kuma sha alwashin jajircewa wajen ganin Obaseki ya zarce a matsayin gwamnan Edo tunda ya dawo jam'iyyar

Tsohon bulaliyar majalisar dattawa kuma shugaban jam'iyyar ADP ta kasa, Roland Owie, a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Owie ya sanar da sauya shekarsa ne a bikin komawarsa jam'iyyar wanda aka yi a garinsu na Ilobi-Isi, kusa da Ehor a karamar hukumar Uhunmwonde ta jihar.

A yayin jawabi, tsohon bulaliyar majalisar ya yi kira ga magoya bayansa da su dage wajen tabbatar da komawar Gwamna Godwin Obaseki kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Dakarun sojin Najeriya sun halaka manyan kwamandoji

Owie ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP tare da tsohon shugaban majalisar, marigayi Chiba Okadigbo.

Tsohon bulaliyar majalisar dattawa, ya koma jam'iyyar PDP
Tsohon bulaliyar majalisar dattawa, ya koma jam'iyyar PDP Hoto: Businessday
Asali: UGC

Bikin da ya samu halartar fitattun shugabannin jam'iyyar PDP daga mazabar Edo ta tsakiya sun samu jagorancin Owere Imasogie, wani jigon jam'iyyar.

Imasogie ya ce fitattun shugabannin jam'iyyar sun tuntubi juna inda suka yanke hukuncin ceto Najeriya.

Ya ce Obaseki wanda ya bayyana a matsayin dan Isi, ya yi babban kokari kuma a saboda haka ne ya cancanci zarcewa.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan

"Na kwashe shekaru sama da 17 ba a gida PDP ba, har sai da na dawo a 2011 da 2015.

"Kusan watanni 15, ina ta tuntubar abokanan siyasa da manyan kasar a kan yadda za mu dawo da kasar nan yadda take. Abinda muka yanke shine dukka iyayen jam'iyyar su koma don sake sabon tsari.

"A don haka, a yau ina kira ga dukkan iyayen jam'iyyar da su dawo gida don yin gyara tare da mayar da Najeriya yadda ya kamata.

"Dawowata jam'iyyar zai tabbatar da ganin cewa Gwamna Obaseki ya zarce."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng