Boko Haram: Dakarun sojin Najeriya sun halaka manyan kwamandoji
Hukumar sojin Najeriya ta ce dakarun rundunar Operation Lafiya Dole sun yi nasarar durkusar da Boko Haram tare da ISWAP a yankin arewa maso gabas.
A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi daga shugaban sashen yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche ya ce bayan bayanan sirrin da suka samu, zakakuran sojojin a ranar 17 ga watan Yuli sun yi niyyar samun 'yan ta'addan a ranar kasuwarsu.
Daga nan ne suka gano kai da kawowarsu a yankin Kolofata, wani gari mai iyaka da Kamaru inda dakarun ke zama.
Sun kashe 'yan ta'adda shida da ke kokarin tsallakawa zuwa Kamaru ta sashen Sambisa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma ce dakarun sun samu bindigogi 3 kirar AK 47, harsasai, mota kirar Honda Salon, babur daya, kekuna takwas, wayoyi uku da layikan waya da Qur'anai biyar.
Ya kara da cewa, "akwai wata wasika da aka rubutawa Abu Fatima, babban kwamandan Boko Haram da wasu takardu.
"Jim kadan bayan samun nasarar aikin, an tabbatar da kashe babban kwamandan Boko Haram Sayinna da wasu mayakan. Ana sanya ran sauran wadanda aka kashe a ciki akwai Imam da Mansur wadanda suke buya a dajin Sambisa," yace.
Ya kara da cewa rundunar ta halaka manyan shugabannin 'yan ta'addan takwas a yayin da suka yi yunkurin shiga sansanin sojin da ke Damasak.
Ya ci gaba da cewa 'yan ta'addan sun hadu da ajalinsu a ranar 2 ga watan Yulin 2020 inda suka samu jagorancin shugabanninsu a Damasak.
KU KARANTA KUMA: Yari ya bayyana yankin da mulkin kasar nan zai koma
Manyan shugabannin Boko Haram da ISWAP da aka kashe a Damasak kuma aka birnesu a kauyen Goski a sa'o'in farko na ranar 3 ga watan Yuli sune:
1. Tumbun Dabino - Ba Issoufou
2. Tumbun Bororo - Amir Batam
3. Tumbun Jaki - Almustapha
4. Tumbun Bagaruwa - Mofou Kollo
5. Dogon Tchoukou - Issah
6. Tumbun Rakke - Mustapha Woulama
7.Tumbun Dila - Boukar Kowa
8.Tumbun Mita - Abou Aisha.
Ya ce, "a jerin nasarorin da aka samu, wasu 'yan ta'addan sun mika makamansu. Sun tabbatar da cewa yanzu ta'addancin na cike da son kudi, mulki, mugunta, ta'addanci da rashin alkibla."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng