Magu: An ci moriyar ganga, an yada ta - Galadima

Magu: An ci moriyar ganga, an yada ta - Galadima

Buba Galadima, tsohon na hannun damar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce tsige Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), da aka yi duk farfaganda ce.

Buhari ya nada Mohammed Umar, tsohon daraktan ayyuka na EFCC, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar bayan dakatar da Magu.

A wata hira da jaridar The Sun, Galadima ya ce maye gurbin Magu da wani shine ake kira da an ci moriyar ganga aka kuma ya da koronta.

Ya yi zargin cewa Magu na ta bin umurnin wasu masu mulki a gwamnati mai ci amma ya take wasu wanda hakan ne ya yi sanadiyar dakatar da shi.

Magu: An ci moriyar ganga, an yada ta - Galadima
Magu: An ci moriyar ganga, an yada ta - Galadima Hoto: Premium Times
Source: UGC

“Ya dade da ya kamata a dakatar da shi. Ya kamata ace an dade da dakatar da Magu daga mukamin amma dalilin da ya sa ya dauki gwamnatin Buhari tsawon shekaru biyar kafin ta tsige shi na iya ba ‘yan Najeriya da dama mamaki, amma a gareni, ba abun mamaki bane,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Magu ya dade a kujerar saboda yana ta yin abunda wasu masu mulki a gwamnatin Buhari suka sa shi yi.

“Amma shakka babu ya take wasu, kuma wannan ne dalilin da yasa suka yanke shawarar yasar da shi.”

Ya ce binciken da ke gudana a yanzu duk farfaganda ce, inda ya yi zargin cewa babu wani abun kwarai da zai fito daga ciki.

KU KARANTA KUMA: El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki

“Na yarda Magu ya yi wa wasu manyan na kewaye da gwamnatin Buhari laifi, kuma wannan ne dalilin da ya sa suka yanke shawarar tsige shi,” in ji shi.

“Ba wai ina kokarin kare Magu bane, bai taba burgeni ba amma kada ‘yan Najeriya su bari a yaudare su da cewar an kori Magu ne saboda jajircewar gwamnatin Buhari wajen yaki da rashawa.

“Kawai an yi amfani da Magu ne domin a sa wa mutane a zukatansu cewa Buhari na yakar cin hanci da rashawa.

“Ku ce na fadi, babu abunda zai fito daga lamarin Magu. Kamar dai kawai suna son nishadantar da mu ne, duk yana daga cikin farfagandar son sanyawa mutane tunanin cewa wannan gwamnatin na yaki da rashawa.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel