Kaduna: Mutanen Tukur-Tukur sun nemi Gwamna ya karbo masu filayensu

Kaduna: Mutanen Tukur-Tukur sun nemi Gwamna ya karbo masu filayensu

Mutanen karkarar Kake, da ke yankin Tukur-Tukur a cikin garin Zaria, sun kai korafi wajen gwamnatin jihar Kaduna, su na rokon a dawo masu da wasu gonakinsu.

Al’ummar Kake ta hannun Malam Shitu Abdullahi Dikko da Alhaji A. Mohammed su na neman gwamnan Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya sa baki a game da halin da su ke ciki.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan mutane sun rubuta takardar korafi ranar 12 ga watan Yuli, 2020 ga mai girma Malam Nasir Ahmed El-Rufai a game da gonakinsu da aka karbe.

A takardar, wadannan Bayin Allah sun gabatar da hujjar mallakar filaye ga gwamnatin El-Rufai, don haka su ka nemi ya sa baki a ba su damar amfani da filayen nomansu.

Masu kukan su na zargin Dagacin unguwar Kake, Mai martaba Malam Yusuf, da wani Basarake a Zaria da hannu wajen raba su da gonakinsu a watannin baya da su ka wuce.

A watan Yuni, wadannan mutane na kauyan Kake, sun kai kara wajen mai girma gwamna, wanda ya yi maza ya bada umarni ga hukumar KASUPDA ta duba lamarin.

KASUPDA ta je wannan yanki, ta zauna da jama’a kuma ta gudanar da bincike kamar yadda aka bukata.

Sai dai kuma bayan gwamnati ta sa baki, Mai garin Tukur-Tukur da jami’an karamar hukuma Zaria sun hana mutanen Kauyen shiga gonakin su domin su yi noma.

“Mun fahimci gwamnati ta bada umarnin dakatar da duk wani aiki a filayen da Marigayi Danisan Zazzau, Alhaji Akilu Idris, tsohon Hakimin Tukur-Tukur, ya raba, har sai kwamiti ya gama aiki.”

KU KARANTA: Saraki ya samu nasara a kotu, Alkali ya ce a maida masa gidajensa

Kaduna: Mutanen Tukur-Tukur sun nemi Gwamna ya karbo masu filayensu
Sarkin Zazzaun Shehu Idris
Asali: Facebook

Wadannan mutane da su ka fito daga karkarar Tukur-Tukur sun ce a dalilin haka, an dakatar da ‘yan kananan manoma da ke aiki a filayen daga shiga cikin gonakinsu.

Manoman sun ce shigar da wannan umarni ga filayen noman da Danisa Akilu Idris bai san da su ba, ya nuna cewa an yaudari gwamnatin jihar wajen daukar matakin da bai dace ba.

Masu karar sun bayyana cewa wasu daga cikin filayen da aka karbe sun shiga hannun masu su ne tun kafin Marigayi Akilu Idris ya zama Hakimin Tukur-Tukur.

Su ka ce: Misali Malam Shitu Abdullahi Dikko ya gaji filin gonarsa ne daga Mahaifinsa Limamin Tukur-Tukur, Malam Abdullahi wanda ya saye filin N4000 a 1983.

Malam Aliyu Tambai ya saye gonarsa ne daga Sarkin Anguwar Bisa a kan N65, 000 a 2003.

Alhaji Dahiru Harande (Danjume) ya saye ta sa gonar ne a kan N12000 a shekarar 1996 a hannun wani Malam Lawal Sadau.

Alhaji Muhammadu Bello (Mai Taya) ya gaji filinsa ne daga Sarkin Tukur-Tukur, Muhammadu Tukur a 1988. Alhaji Mohammed ya saye gonarsa ne a 2007.

Malam Musa Abeku ya saye filinsa ne a 2003 hannun Gora Emma Tabat kan N210, 000. Shi kuma Tabat ya saya ne daga hannun Abdullahi Danlaure na Anguwar Iya tun 2002.

Yanzu an bada umarnin dakatar da amfani da duk wadannan filaye sai an gama bincike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel