Benzema da fitattun ‘Yan wasan Real Madrid da su ka yi tashe a La-ligar 2020

Benzema da fitattun ‘Yan wasan Real Madrid da su ka yi tashe a La-ligar 2020

- Kungiyar Real Madrid ta lashe gasar La-liga na shekarar 2019/2020

- Mun kawo jerin ‘Yan wasan da su ka yi wa kungiyar kokari sosai

- Zinedine Zidane ya na da hannu a nasarar da Real Madrid ta samu

Ganin cewa an tabbatar da Real Madrid a matsayin zakarun 2019-20 na gasar La-liga a kasar Sifen, Legit.ng Hausa ta Ambato ‘yan kwallon da su ka yi abin a-zo-a-gani a bana.

Real Madrid ta juya wasannin kakar bana kamar ba za ta kai labari ba, bayan ta sha kashi a Turai a hannun Manchester City. Amma daga baya abubuwa sun sauya zani a Madrid.

Su wane ‘yan wasan ne su ka yi wa Real Madrid kokari wajen lashe kofi a shekarar nan:

1. Thibaut Courtois

‘Dan wasa mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois bai yi kasa a gwiwa a bana ba. Bajintar ‘dan kwallon ta jawowa Real Madrid a wasanni da-dama. Golan ya shafe wasanni kusan 20 ba a zura masa kwallo a raga ba – abin da babu wanda ya yi a bana.

KU KARANTA: La-liga ta dawo Real Madrid, Barcelona ta sha kashi a hannun Osasuna

Benzema da fitattun ‘Yan wasan Real Madrid da su ka yi tashe a La-ligar 2020
Zinedine Zidane Hoto: Real Madrid
Asali: Getty Images

2. Karim Benzema

Karim Benzema ya zurawa Real Madrid kwallaye 20 a raga a La-ligar bana. Lionel Messi ne kurum ya sha gaban ‘dan wasan gaban. Bayan haka Benzema ya yi sanadiyyar cin kwallaye takwas. Bafaranshen ya nuna kansa a gasar wannan shekara.

3. Sergio Ramos

Sergio Ramos ‘dan wasan baya ne mai kamar ‘dan gaba wanda ya ci finaritinsa ta 20 a jere a wasan Real Sociedad, wannan ya sa ya zama ‘dan bayan da ya fi kowa kwallaye a tarihin La-liga. Ramos mai kwallaye 10 ya yi wa Real Madrid namijin kokari a gasar.

Ba zai yiwu a ambaci nasarar Real Madrid ba tare da an kira kocin kungiyar, Zinedine Zidane da kuma ‘yan kwallo irinsu Raphael Varane, Luka Modric da Caseimero ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng