Kotu ta bada umarnin EFCC ta maidawa Saraki wasu gidajensa da aka karbe a Kwara

Kotu ta bada umarnin EFCC ta maidawa Saraki wasu gidajensa da aka karbe a Kwara

A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020, babban kotun tarayya da ke Legas ta zauna game da shari’ar da ake yi tsakanin Bukola Saraki da hukumar EFCC.

Kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta maida wasu gidaje biyu da aka karbe daga hannun tsohon shugaban majalisar dattawan.

Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa ya maidawa tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki gidajen na sa ne yayin da ya ke yanke hukunci a jiya.

A Disamban 2019, EFCC ta yi nasarar farko a kotu, aka ba hukumar damar rike wasu gidajen fitaccen ‘dan siyasar da ke cikin garin Ilorin a jihar Kwara.

Kotu ta ba EFCC wadannan gidaje ne bayan hukumar ta bayyana yadda aka mallaki kadarorin da kudin gwamnati a lokacin da Bukola Saraki ya ke gwamna.

Saraki ya rike gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Ba da kudin sata Saraki ya mallaki gidansa ba

Kotu ta bada umarnin EFCC ta maidawa Saraki wasu gidajensa da aka karbe a Kwara
Bukola Saraki Hoto: NASS
Asali: Twitter

Yunkurin da EFCC ta yi na ganin cewa wadannan gidaje sun dawo hannunta na din-din-din ya ci tura, inda Bukola Saraki ya kalubalanci gwamnatin tarayyar.

Mai shari’a Rilwan Aikawa ya ce bai samu wata hujja mai gamsarwa da za ta sa kotu ta bar wa hukumar EFCC wadannan gidaje ba.

Alkalin ya ke cewa: “Babu wata hanya da za a bi a mallakawa EFCC gidajen har abada.”

Lauyan da ya tsayawa EFCC, Olamide Sadiq, ya ce: “Yayin da ake bincike, mun bankado wasu ciniki da su ka sabawa ka’ida da aka yi”

“Bincikenmu ya nuna mana cewa a lokacin da Dr. Olubukola Abubakar Saraki ya ke gwamnan Kwara, bayan an biya jihar daga asusun FAAC, a kan ajiye akalla N100m a asusun gidan gwamnati.”

Hukumar EFCC ta ce da haka Saraki ya mallaki gidajen na sa a Ilorin.

Lauyan Saraki, Kehinde Ogunwumiju (SAN), ya karyata wannan zargi da ya ce yunkurin bata tsohon gwamnan ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel