Magu ya wanke Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Falana daga zargi

Magu ya wanke Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Falana daga zargi

- Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya yi magana game da jita-jitar da ke yawo a kansa

- Ana zargin cewa Magu ya ba Mataimakin shugaban kasa da wasu mutane Biliyoyi

- Tsohon shugaban hukumar EFCC ya karyata wannan zargi ta bakin wani Lauyansa

Kusan sa’a 24 bayan samun ‘yanci, Ibrahim Magu ya rubuta takarda ga kwamitin shugaban kasa da ke binciken zargin badakala a EFCC, inda ya kare kansa.

Gidan talabijin na Channels TV ya bada rahoto cewa tsohon shugaban hukumar ta EFCC, ya rubuta takardarsa ne zuwa ga shugaban kwamitin bincike, Ayo Salami.

Ibrahim Magu ta bakin lauyansa, Wahab Shittu ya bayyana zargin cewa ya ba mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Naira biliyan 4 a matsayin karya.

Haka zalika shugaban na EFCC da aka dakatar ya ce babu gaskiya a maganar da ke yawo cewa ya biya fitaccen lauyar nan Femi Falana SAN, Naira miliyan 28.

Lauyan ya bayyana cewa wadannan duk labaran karya ne da ake yadawa domin a bata sunan mataimakin shugaban kasa, Ibrahim Magu da kuma Femi Falana.

KU KARANTA: Jami'ai sun shiga ofishin Magu, sun yi awon gaba da wasu kaya

Magu ya wanke Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Falana daga zargi
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Ta bakin Shittu, Magu ya musanya zargin ya na da alaka da wani ‘dan kasuwan canji a Kaduna.

A na su bangaren, tuni mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Femi Falana su ka musanya zargin karbar wasu kudi daga shugaban hukumar EFCC.

Game da gidansa da aka shiga aka yi bincike a ranar 6 ga watan Yuli, Magu ya hakikance a kan cewa babu wani abin zargi da aka samu a cikin gidan.

Ko da kayan alatu, ko daloli da agogo ba a samu a gidan ba. Lauyan ya ce binciken gidan bai sa an samu wasu hujjoji a kan tsohon shugaban hukumar na EFCC ba.

Bugu da kari, Wahab Shittu ya bayyana cewa motocin da aka cire daga gidan, wadanda hukumar ta ba Magu ne a matsayinsa na mukaddashin shugaba.

Sai dai Lauyan ya koka da cewa ba su samu takardar zargin da ake tuhumar mai gidansa da su ba. Ya ce da zarar sun samu, Magu zai wanke kansa, kuma ya bukaci ayi adalci a binciken.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel