Gwamnonin jam'iyyar APC sun gudanar da muhimmin taro a kan zaben Edo

Gwamnonin jam'iyyar APC sun gudanar da muhimmin taro a kan zaben Edo

Gwamnonin APC da aka dorawa alhakin yakin neman nasarar jam'iyyar a zaben gwamnan jihar Edo sun gudanar da muhimmin taro domin tattauna hanyoyin da zasu bi domin cimma burinsu a zaben da za a yi ranar 10 ga watan Satumba.

Gwamnonin sun gudanar da taron ne a wani wuri da ba a bayyana ba, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa wata majiya a hedikwatar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) a Abuja ta tabbatar mata.

Ana tunanin sun shiga taron ko kuma zasu zauna a wani lokaci nan gaba a daren nan.

Kafin samun labarin taron gwamnonin, mambobin wani kwamitin yakin neman zaben APC a Edo, sun shafe fiye da mintuna 45 suna tattaunawa a hedikwatar jam'iyyar APC, kafin daga bisani su sauya muhalli zuwa wani gida a cikin Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kwamitin, gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, da mataimakinsa Ovie Omo-Agege; da Farfesa Julius Ihonvibere da sauransu.

Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC; Fasto Osagie Ize-Iyamu, da dan takarar mataimaki, Gani Audu, suna wurin taron.

Gwamnonin jam'iyyar APC sun gudanar da muhimmin taro a kan zaben Edo
Gwamnonin jam'iyyar APC yayin wata ziyarar Tinubu
Asali: Twitter

Mambobin kwamitin da Ize-Iyamu sun ki yin magana da manema labarai bayan fitowarsu daga hedikwatar jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya kaddamar da cinikayyar gwal, mutane 250,000 zasu samu aiki

Wata majiya ta gano cewa sun bar hedikwatar jam'iyyar APC ne domin ganawa da wasu ma su ruwa da tsaki domin kara tattauna yadda za a karbi jihar Edo daga hannun jam'iyyar PDP.

"Taronmu a hedikwatar jam'iyyar APC takaitacce ne saboda akwai bukatar mu gana da wasu manyan ma su ruwa da tsaki a harkar zaben gwamnan jihar Edo domin tattaunawa dasu," a cewar wata majiya.

The Nation ta rawaito majiyarta na cewa; ''zaben jihar Edo ya na da matukar muhimmanci ga jam'iyyar APC, a saboda hakane gwamnonin za su gudanar da muhimmin taro a wani wuri a unguwar Asokoro.

"Za su tattauna yadda jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben gwamnan Edo da Ondo," a cewar majiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel