Mutum 6 za su maimaita hidimar kasa a Kano - NYSC

Mutum 6 za su maimaita hidimar kasa a Kano - NYSC

- Hukumar NYSC a jihar Kano za ta tilastawa mutum shida su maimaita shekara daya ta bautar kasa a jihar

- Hajiya Aisha Mohammad, shugabar hukumar NYSC ta jihar ce ta sanar da wannan labarin kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito

- A cewarta laifinsu dai shi ne rashin tsayawa su kiyaye dokokin da hukumar ta shar'anta musu

A ranar da wasu ke farin ciki na kammala bautar kasa ta NYSC, wasu ko murnarsu ta koma ciki a sakamakon wajabta musu maimaita shekara daya ta bautar da za su yi a jihar Kano.

Hajiya Aisha Mohammad, shugabar hukumar NYSC ta jihar Kano, ita ce ta bada wannan sanarwa a yayin bikin yaye rukuni na biyu na masu hidimar kasar da suka kammala a bana.

Aisha ta bayyana cewa, mutanen shida ne za su maimaita shekara guda ta bautar kasa, yayin da kuma hukumar ta tsawaita hidimar wasu mutum 16 sakamakon laifuka iri-iri da suka aikata.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an yi bikin gabatar da takardun shaidar kammala bautar kasar wanda aka gudanar a sakateriyar hukumar da ke kan titin Gwarzo a kanon Dabo.ano State.

Ta bayyana cewa, matasa 2,677 ne suka kammala bautar kasarsu salin alin a jihar Kano ba tare da samun wata tangarda ba.

Masu bautar kasa NYSC
Hoto daga Premium Times
Masu bautar kasa NYSC Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

Shugaban hukumar ta ce duk cikin masu bautar kasar babu wanda cutar korona ta harba har suka kammala hidimarsu ta tsawon shekara guda a jihar.

Ta kara da cewa tuni hukumar ta yi tanadin duk wasu shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da komawar masu bautar kasar zuwa jihohinsu na asali cikin aminci.

Ta gargade su a akan su tabbatar sun kasance sanye cikin kakin da hukumar ta basu na hidima yayin da zasu koma gidajen su.

KARANTA KUMA: Kungiyar Musulmi za ta buɗe sabuwar Jami'a a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, ya jagoranci wani taro na yanar gizo inda ya kaddamar da shirin fadar shugaban kasa na bunkasa hakar gwal (PAGMDI).

Legit.ng ta ruwaito cewa, shirin PAGMDI zai samawa 'yan Nigeria akalla 250,000 ayyuka, yayin da gwamnatin tarayya za ta rika samun kudaden shiga $500m a kowacce shekara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina ya fitar, ya ce shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da kuma baiwa Nigeria kwarin guiwar samun makoma mai kyau a nan gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng