'Yanta mayakan Boko Haram 602: Sai da mu ka rantsar dasu kafin sakinsu - DHQ

'Yanta mayakan Boko Haram 602: Sai da mu ka rantsar dasu kafin sakinsu - DHQ

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta ce tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram sun yi rantsuwa cewa zasu zama ma su biyayya ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

DHQ ta bayyana cewa ta dauki tsawon makon jiya ta na rantsar da tubabbun mayakan bayan kammala basu horon saisaita tunaninsu da kuma gyaran halayensu (DDR).

Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke jawabi a kan atisayen rundunar4 soji a tsakanin 9 ga watan Yuli zuwa 16 ga wata.

Janar Enenche ya bayyana cewa an bawa tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram horo daban - daban a karkashin atisayen 'SAFE CORRIDOR'.

Kazalika, ya ce sun barranta kansu da zama mambobin kungiyar Boko Haram bayan sun mika wuya.

A cewar Janar Enenche, bayan an kammala basu horo a sansanin Malam Sidi, tubabbun mayakan sun yi rantsuwa a gaban kwamitin alkalai mai mutane 11.

"Dalilin rantsar dasu shine domin tabbatar da shahadarsu, biyayya, da yin da'a da biyayya ga gewamnatin tarayyar Najeriya.

'Yanta mayakan Boko Haram 602: Sai da mu ka rantsar dasu kafin sakinsu - DHQ
Tubabbun mayakan Boko Haram
Asali: UGC

"Manufar yin hakan ita ce; su san cewa idan su ka kara yin wani laifi nan gaba, za a janye duk wani rangwame sanna a tuhumesu da aikata laifi ga kasa.

"Ya zuwa yanzu rundunar soji ta kammala bayar da horo ga jimillar tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 882 a karkashin atisayen SAFE CORRIDOR.

DUBA WANNAN: Yadda shirin PAGMDI zai samar da aiki ga 'yan Najeriya 250,000 - Buhari

"An saki tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 280 a rukuni na farko.

"Babu rudani a cikin sakon da DHQ ke aikawa sauran 'yan ta'adda; su mika wuya, su samu damar morar DDR," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel