Bunkasa Almajirci: Jihar Gombe zata karrama mahaddatan Al-Qur'ani da satifiket

Bunkasa Almajirci: Jihar Gombe zata karrama mahaddatan Al-Qur'ani da satifiket

- Gwamnatin jihar Gombe ta daura damar bunkasa tsarin karin Almajiranci a jihar

- Gmamnatin jihar ta shirya fara bada satifiket ga almajiran da suka haddace Al-Qur'ani mai girma

- Jihar ta tabbatar da wannan kudirin nata ta hanyar hadin guiwa da hukumar kula da harkokin karatun Arabi da addinin Musulunci ta kasa

Gwamnatin jihar Gombe ta shirya fara bada takardun karramawa na satifiket daga hukumar kula da harkokin karatun Arabi da addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) ga mahaddata Al-Qur'ani mai girma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Dr. Abdullahi Bappah Ahmad Garkuwa, ko-odinetan shirin samar da nagartaccen ilimi ga kowa na jihar Gombe (BESDA).

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Usman Dankyarana, mai tallafawa kodinetan shirin a Bauchi ya ce makasudin yin hakan shine gayyatar Almajirai zuwa ga wani taron baje kolin fasaha da kuma neman hadin guiwar hukumar wajen bada satifiket ga daliban da suka haddace Al-Qur'ani a makarantun tsangaya.

A cewar Dr. Garkuwa, almajiri zai samu damar ci gaba da karatunsa a manyan makarantun boko da ke a fadin kasar, ta hanyar amfani da wannan shaidar kammala karatun Al-Qur'ani.

Ya ce kuma gwamnatin jihar Gombe a bangarenta ta daura damarar bunkasa karatun allo a jihar.

Kodinetan shirin ya kuma fayyace shirin gwamnati na gina makarantun tsangaya na zamani guda 11 wadanda kowacce makaranta zata dauki dalibai 1000 a kowacce karamar hukumar jihar.

Bunkasa Almajirci: Jihar Gombe zata karrama mahaddatan Al-Qur'ani da satifiket
Bunkasa Almajirci: Jihar Gombe zata karrama mahaddatan Al-Qur'ani da satifiket Source: Twitter
Asali: Original

A wani labarin makamancin wannan, wata yarinya mai shekaru 8 da haihuwa, Nuroh Nasir, ta samu nasarar lashe gasar karatun Al-Qur'ani da Hadisi, da kungiyar Faith Unites Muslim Charity Initiative (FUMCI) ta shirya na rukunin shekarar 2019.

Wakilin Legit.ng, Ibrahim Akinola, a rahotonsa, ya bayyana cewa yarinyar ta samu nasara ne akan sauran abokan karawarta guda tara a bangaren Al-Qur'ani inda ta zama zakara yayin da ta lallasa abokan karawarta guda hudu a bangaren Hadisi, a ranar karshe ta kammala gasar da ya gudana a babban garin Lagos.

Taron rufe gasar ya samu halartar manyan malaman addinin Musulunci daga jihar da suka hada da kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Lagos da kuma Amirul Hajj na shekarar 2019, Abdul-Hakeem Abdul-Lateef, wanda ya jinjinawa daliban da iyayensu bisa namijin kokarinsu na tsunduma cikin harkokin karatun addini.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya aike da sakon gargadi ga iyayen da suka tura yaransu karatun Almajiranci.

Gwamnan ya ce duk wani magidanci da ya yi kunnen uwar shegu da sakonsa zai karkare a gidan kaso.

Ya bayar da wannan gargadin ne a ranar 25 ga watan Mayu, a lokacin da ya ziyarci wasu almajirai da aka maidosu Kaduna daga jihar Nasarawa, da kuma suke samun kulawa da bunkasar rayuwa a kwalejin gwamnati dake Kurmin Mashi, Kaduna.

Gwamnan ya ce duk wani malamin addinin da ya dauki wani dalibi a makarantar allo zai fuskanci hukuncin dauri da kuma tarar N100,000 ko N200,000 ga kowanne dalibi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng