Nadin Ciroma da Dan-Agundi: Ganduje ya yi martani a kan zargin hannunsa a ciki

Nadin Ciroma da Dan-Agundi: Ganduje ya yi martani a kan zargin hannunsa a ciki

Gwamnatin jihar Kano ta yi martani game da zargin gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje da ake yi da hannu a cikin sake nada wasu mambobi biyu a majalisar masarautar Kano.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, masarautar Kano ta rubuta wasika wacce take neman izini daga gwamnan jihar don sake nada wasu mutum biyu a majalisarta.

Sune Ciroman Kano, Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Wamban Kano da tubabben Sarkin Dawaki Maituta, Aminu Babba Dan Agundi a matsayin sabon Sarkin Dawaki Babba.

A yayin martani a kan lamarin, mazauna jihar Kano sun fusata da wannan ci gaban inda suka yi zargin cewa gwamnan ya taba neman Muhammadu Sanusi II da ya dawowa da Babba Dan Agundi rawaninsa amma ya ki.

A martaninsa, babban mai bai wa gwamnan shawara a kan harkokin sarauta, Tijjani Mailafiya Sanka, ya ce wannan zargin ba gaskiya bane kuma bashi da tushe.

Ya ce wadanda ke cece-kuce a kan zancen mutane ne da ke son rashin zaman lafiya fiye da sasanci da kuma yafiya.

Nadin Ciroma da Dan-Agundi: Ganduje ya yi martani a kan zargin hannunsa a ciki
Nadin Ciroma da Dan-Agundi: Ganduje ya yi martani a kan zargin hannunsa a ciki Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Ni ne da kaina ke tsakanin gwamnatin da fadar kuma zan iya tabbatar muku da cewa hakan bai taba faruwa ba.

"Ba abun yarda bane idan aka ce zababben gwamnan zai roki sarkin don yin wani abinda shari'a bata hana ba amma ya ki amincewa dashi," yace.

Sanka ya ce duk masu cewa sarkin ya yanke shawarar da mahaifinsa ba zai so ba suna fadin hakan ne a rashin sani.

Ya ce wannan ba shine karo na farko ba da ake tube rawanin hakimi a kan wani laifi da ake zarginsa da shi ba sannan kuma a mayar masa.

KU KARANTA KUMA: Abinda diyata ta sanar dani kafin mutuwarta - Mahaifin marigayiya Arotile

"A zamanin Ado Bayero, an tube rawanin Wamban Kano, Abubakar, kuma daga baya an nada shi a matsayin Dan Buram.

"Don haka wannan ba sabon abu bane kuma sarkin ya bi sahun mahaifinsa ne.

"Hakazalika, a lokacin Sarkin Kano Usma, Galadiman lokacin Mahmud, an tube masa rawani saboda wani laifi amma daga bisani an mayar da shi Magajin Gari," ya kara da cewa.

Sanka ya ce mutum biyun da aka yi wa nadi an duba tsananin gogewarsu ne a mulki da kuma sanin da suke da shi na abubuwan da ke faruwa a halin yanzu.

Ya ce hakan ne ya sa ake kwadayin karuwa da gogewarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng