Abinda diyata ta sanar dani kafin mutuwarta - Mahaifin marigayiya Arotile

Abinda diyata ta sanar dani kafin mutuwarta - Mahaifin marigayiya Arotile

Akintunde Arotile, mahaifin marigayiyar matukiyar jirgin yaki ta farko a rundunar sojin saman Najeriya, ya yi bayanin yadda ya yi magana da diyarsa sa'o'i kadan kafin mutuwarta.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Arotile ya ce ya matukar girgiza idan ya tuna cewa Tolulope ta so zama sojan sama tun tana karama.

Marigayiyar sojan ta rasu ne sakamakon hatsarin mota a Kaduna a ranar Talata, 15 ga watan Yuli.

Wani tsohon dan ajinsu ne ya bigeta da mota ba tare da sani ba inda ta samu raunika a kanta, jaridar The Cable ta ruwaito.

Arotile ya tuna yadda ya sanar da diyarsa cewa ta dawo gida da wuri a yayin da suke magana sa'o'i kadan kafin rasuwarta.

Abinda diyata ta sanar dani kafin mutuwarta - Mahaifin marigayiya Arotile
Abinda diyata ta sanar dani kafin mutuwarta - Mahaifin marigayiya Arotile Hoto: Expressive Info
Asali: UGC

Abinda bai sani ba shine ba za ta dawo gida ba kwata-kwata har abada.

"A jiya wurin karfe 1:00 na rana na kirata saboda bata dade da dawowa daga Katsina ba wurin aiki. An bata hutun mako daya," yace.

"Toh tana bacci amma ta sanar dani cewa tana dan hutawa ne. Za ta fita anjima don duba wasu takardu. Na ce mata kada ta dade ta dawo gida da wuri saboda a wurin diyata ta farko take zama a Kaduna.

"Wurin karfe 5:30 na yamma, wani ya kirani inda ya tambayeni cewar ko na kirata yau, sai nace masa eh, sai yace in kirata amma ba a daga wayarta. Na kira abokan aikinta amma sai naji suna ta kuka a waya.

"Na bukaci sanin me ke faruwa amma sai kuka suke yi. Na kira daya daga cikin iyayen gidanta amma sai yace tana ma'adanar gawawwaki.

"Na ce mishi ban yarda ba saboda ban dade da yin magana da ita ba. Ya ce babu shakka rasuwa tayi."

Ya tuna yadda diyarsa ta ke son zama matukiyar jirgin sama inda ya ce ba kokari kadai gareta ba, tana da abubuwan bada mamaki.

"Wata rana lokacin tana karama, ta nuna min wani jirgi inda tace za ta tuka shi idan ta girma. Daga nan ta fara kokarin ganin tabbatar mafarkinta. Nagode Allah ta cimma burinta kafin mutuwarta" yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel