Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya fadi bayan sakinsa

Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya fadi bayan sakinsa

Bayan ya kwashe kimanin kwanaki 10 a tsare, Ibrahim Magu ya samu yancinsa a yammacin ranar Laraba, 15 ga watan Yuli.

Jim kadan bayan sakinsa dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya zanta da jaridar The Nation.

Legit.ng ta zakulo wasu muhimman abubuwa hudu da tsohon shugaban na EFCC ya fadi a jawabinsa.

1. Zargin da ake masa duk marasa tushe ne

Magu ya ce yayi matukar mamaki da ya karanta jerin zargin da ake masa, wadanda ya bayyana a matsayin marasa tushe.

Kamar yadda yace, an hada jerin zargin ne don a bata masa suna da na EFCC.

Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya fadi bayan sakinsa
Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya fadi bayan sakinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

2. Kura ta ci kura

Magu ya ce abinda ya faru da shi shine ake kira da "kura ta ci kura". Sai dai kuma ya dauki hakan a matsayin daya daga cikin hadarurrukan da ke tattare da aikin nasa.

3. Za a iya nasara da yaki da rashawa

Dakataccen shugaban hukumar EFCC ya ce komai kalubalen da zai fuskanta, ya yarda cewa za a yi nasara a yaki da rashawa.

A don haka yayi kira ga 'yan Najeriya da su bada goyon baya a kan yaki da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa gaba.

KU KARANTA KUMA: Nan bada dadewa ba za a rasa ma su karfin gwuiwar yaki da cin hanci - Osinbajo

4. Bai girgiza da abinda ya faru da shi ba, yace yana farin cikin sakinsa da aka yi

Magu ya ce wannan abun da ya faru da shi ba shi ake yaka ba, rashawa ake yaka.

"Ina farin ciki da fitowata kuma na yarda akwai nasara."

A halin da ake ciki, fadar shugaban kasa Muhammadu ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shugaban kasa ba zai samu rashin kwarin guiwa ba a kan yaki da rashawa da yake yi.

Ta bayyana hakan ne saboda kalubalantar sa da abokai hamayya ke yi. Ta ce ya riga ya shirya ganin bayan rashawa a kasar nan.

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu, wanda ya sanar da wannan matsayar yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a Abuja, ya yi martani ne ga jam'iyyar PDP bayan fara bincikar Ibrahim Magu.

Ya ce yanayin gwagwarmaya da shugaban kasar ke yi da kuma yaki da rashawa ya nuna yanayin abinda PDP ta bari bayan kammala wa'adin mulkinta.

Shehu ya ce rashawa ta zama tamkar ba laifi ba ga PDP, lamarin da yasa suka kasa bambamcewa tsakanin rashawa da sata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng