Cutar korona ta hallaka shugaban kungiyar kwadago, Kwamred Gambo

Cutar korona ta hallaka shugaban kungiyar kwadago, Kwamred Gambo

Cutar korona ta hallaka Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Taraba, Kwamred Peter Gambo, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

A cewar jaridar, Kwamred Gambo ya mutu ne da safiyar ranar Laraba bayan gajeriyar jinya a asibitin kwararru da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kwamishinan lafiya a jihar Taraba, Dakta Innocent Vakkai, ya tabbatar da mutuwar Kwamred yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Jalingo.

Sai dai, Vakkai ya musanta rahotannin da suka alakanta mutuwar Kwamred Gambo da annobar cutar korona.

A cewar kwamishinan, duk da an kwantar da Kwamred Gambo a asibitin, sakamakon gwajinsa bai nuna cewa ya kamu da cutar korona ba.

A ranar Talata ne cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta sanar da cewa akwai jimillar mutane 33,616 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar korona a Najeriya.

Ya zuwa ranar Talatar, an sallami mutane 13,792 daga cibiyoyin killacewa da ke fadin kasa bayan an tabbatar da cewa sun warke sarai. Kazalika, cutar ta hallaka jimillar mutane 754 a Najeriya.

A wani labarin daban, hukumar kula da filayen jirgin sama mallakar gwamnatin Najeriya (FAAN) ta yi 'Alla-wadai' da halayyar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya nuna a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu da ke birnin Kano.

Cutar korona ta hallaka shugaban kungiyar kwadago, Kwamred Gambo
Wasu shugabannin kungiyar kwadago (NLC)
Asali: Twitter

Ana zargin tsohon gwamna Yari da karya dokar da gwamnatin tarayya ta saka bayan bude filayen jirgi domin cigaba da jigilar fasinjoji a iya cikin Najeriya sakamakon sassauta dokar kulle a mataki na biyu.

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamna Umahi na jihar Ebonyi zai bude makarantu a watan Agusta

Tun kafin a bude filayen jirgin sama, gwamnatin tarayya ta sanar da jerin wasu matakai da fasinjoji da kamfanonin jirage zasu yi wa biyayya domin dakile yaduwar annobar korona.

A cikin sanarwar da FG ta fitar, ta bakin ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika, ta ce babu batun wasu shafaffu da mai ko manyan mutane (VIPs) wajen tabbatar da cewa an yi aiki da dokoki da shawarwarin gwamnati a kan kowanne fasinja.

A cikin wani sako da FAAN ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Tuwita, ta yi 'tir' da halayyar Yari ta wofantar da dokar FG wacce ta bukataci a yi aiki da ita a kan kowanne fasinja a filin jirgin sama na kasa da aka bude.

FAAN ta zargi Yari da yin amfani da karfin tuwo wajen ture jami'inta a yayin da ya ke kokarin ganin an yi wa jakar tsohon gwamnan feshin sinadarin da ke kashe kananan kwayoyin cuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel