Kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a Edo ya yi zama a jihar Ribas

Kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a Edo ya yi zama a jihar Ribas

A ranar Laraba, jaridar The Nation ta rahoto cewa jirgin yakin jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo, ya sha alwashin samun nasara a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar PDP ta na kokarin ganin tazarcen gwamna Godwin Obaseki ya tabbata a zaben da za a fafata a ranar 19 ga watan Satumban 2020.

Kwamitin da PDP ta kafa domin yakin zabe ya yi zama a farkon makon nan a gidan gwamnatin jihar Ribas. Manyan jam’iyyar sun yi wannan zama ne a bayan labule.

Jam’iyyar PDP bayan ta duba irin ayyukan cigaban da gwamnatin Godwin Obaseki ta yi a jihar Ribas, ta ce ‘dan takarar na ta ya sha gaban sauran masu neman mulkin jihar.

A wani jawabi da gwamnatin Ribas ta fitar yau ta bakin kwamishinan yada labarai da sadarwa, Paulinus Nsirim, ta ce mutanen Edo za su so gwamna mai-ci ya zarce.

Gwamnatin jihar Ribas ta ce mutanen jihar za su yi kokarin ganin sun cigaba da samun romon da gwamna Godwin Obaseki ya kawo masu har zuwa shekarar 2024.

KU KARANTA: Zaben 2020: Akwai Gwamnonin APC da ke tare da ni - Obaseki

Kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a Edo ya yi zama a jihar Ribas
Gwamnan jihar Ribas
Asali: UGC

Wanda ya jagoranci wannan zama da aka yi shi ne shugaban yakin neman zaben, Nyesom Wike. Sauran gwamnoni da shugabannin kananan kwamiti sun halarci taron.

Gwamnoni irinsu Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Mankinde, su na cikin wanda aka yi wadanda aka yi taron da su.

Gwamna Ahmadu Fintiri wanda shi ne mataimakin kwamitin neman zaben, ya yi magana, ya ce sun fito da tsarin da ‘za mu cigaba da rike abin da PDP ta mallaka.’

Ya ke cewa: “Zaben ya riga ya zo gaban teburin PDP. Mu na da ‘dan takarar da ya ke da dadin tallatawa, shi ne Gwamna Godwin Obaseki.”

“Abin da ke kasa shi ne, Edo jihar PDP ce saboda a zaben 2019 da ya gabata, mun ci ko ina. Saboda haka ba abin mamaki ba ne don gwamna Obaseki ya sauya-sheka, daga APC ya dawo cikinmu.”

Fintiri ya kara da cewa: “Yanzu mu na hada karfi da karfe, kuma babu abin da ya rage. Edo jihar PDP ce gaba daya, kuma za mu ci zabe.” Bayan nan jigon PDP, Raymond Dokpesi ya yi magana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel