Buhari zai yi nasara a yaki da rashawa - Fadar shugaban kasa
Fadar shugaban kasa Muhammadu ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa shugaban kasa ba zai samu rashin kwarin guiwa ba a kan yaki da rashawa da yake yi a saboda kalubalantar sa da abokai hamayya ke yi.
Fadar shugaban kasar ta ce Buhari ya riga ya shirya ganin bayan rashawa a kasar nan.
Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu, wanda ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, ya yi martani ne ga jam'iyyar PDP bayan fara bincikar Ibrahim Magu.
Ya ce yanayin gwagwarmaya da shugaban kasar ke yi da kuma yaki da rashawa ya nuna yanayin abinda PDP ta bari bayan kammala wa'adin mulkinta.
Shehu ya ce rashawa ta zama tamkar ba laifi ba ga PDP, lamarin da yasa suka kasa bambamce tsakanin rashawa da sata.
Kakakin shugaban kasar ya jinjinawa gwamnatin ubangidansa a kan yadda take ganin bayan rashawa a kasar.
"Yawan wadanda ake bincika a kan rashawa, sabbi da tsoffi na damun shugaban kasa. Jam'iyyar da ta kammala mulki ta bar baya da kura don bata bincike ko hukunta su," yace.
Shehu ya yi kira ga PDP da su bari a yi bincike tare da gurfanarwa a maimakon surutun da suke.
KU KARANTA KUMA: Zargin lalata: Ministan Buhari ya yi martani
Ya bayyana cewa, akwai tabbacin sashen shari'ar kasar nan zai yi iyakar kokarinsa.
"Gwamnatin yanzu tana shawo kan matsalolin da PDP ta kasa kuma ga sabbi na tasowa," ya sanar.
A wani labarin, mun ji cewa a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, an ci gaba da bincikar dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a gaban kwamitin fadar shugaban kasa.
An zargesa da yin amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba tare da damfara.
Bayan komawar binciken kwamitin, manyan jami'an hukumar da daraktoci sun hallara gaban kwamitin inda suka ci gaba da bayani.
A cikin binciken, an kwace wasu motoci biyu na ofishin dakataccen shugaban EFCC.
An samo daya a Abuja inda dayar aka samota daga Maiduguri. An ajiye su a hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng