‘Yan Sanda sun kama Faston da ake zargi da amfani da Yarinya a jihar Ogun

‘Yan Sanda sun kama Faston da ake zargi da amfani da Yarinya a jihar Ogun

- ‘Yan Sanda sun kama Fasto Oketokun Abiodun da laifin yi wa wata fyade

- Ana tuhumar wannan mutum da laifin lalata da wata yarinya a garin Odeda

- Faston ya amsa laifinsa, kuma ana sa ran gurfanar da shi nan gaba a kotu

Wani Fasto da ke aiki da cocin ‘Light Christian Church’ da ke karamar hukumar Odeda, a jihar Ogun, ya shiga hannun dakan ‘yan sanda bisa zargin lalata da karamar yarinya.

Jaridar Punch ta ce ‘yan sanda sun cafke Fasto Oketokun Abiodun mai shekara 59 a Duniya, su na zargin cewa ya yi lalata da wata yarinya mai shekara 10 da haihuwa.

Wannan limamin coci ya yi nasarar kai karamar yarinyar cikin dakinsa da rana tsaka, inda ya samu damar tarawa da ita da karfi da yaji.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, a wani jawabi da ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wannan mutumi da ake zargi da laifi a ranar Asabar.

Jawabin ya ce: “An kama faston ne bayan kukan da mahaifin wannan yarinya ya kai a ofishin ‘yan sanda da ke Odeda.”

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wani 'Dan luwadi hukuncin daurin shekaru 2 a kurkuku

‘Yan Sanda sun kama Faston da ake zargi da amfani da Yarinya a jihar Ogun
Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Ogun
Asali: UGC

“Wanda ya kawo karar ya ce faston ya hangi yarinyar ta na wasa ne da sauran yara, sai ya kira ta, ya aiketa ta kawo masa mubudin dakinsa.”

“A lokacin da wannan ‘yar yarinya da ba ta san komai ba ta kama hanya, sai ya bita cikin daki, ya danneta a kan gado, ya rufe mata baki, ya yi amfani da ita.”

Bayan ‘yan sanda sun samu wannan labari, sai jami’i CSP Ajayi Williams ya bada umarnin a kamo wannan fasto mai aikin assha, kuma aka yi ram da shi din.

Da aka tsare shi, Oketokun Abiodun ya amsa laifinsa, a dalilin haka aka rufe shi. Ita kuma yarinyar ta na babban asibitin garin Odeda, inda ake kula da lafiyarta.

Abimbola Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin a maida wanda ake zargin zuwa CID domin kara bincike, a kuma gurfanar da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel