Jami'an 'yan sanda 7 sun rasa ransu a jihar Katsina

Jami'an 'yan sanda 7 sun rasa ransu a jihar Katsina

- Rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwar mutuwar wasu jami'anta guda bakwai sakamakon hatsarin mota da ya ritsa dasu

- Hatsarin mota ya ritsa da jami'an ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina domin yaki da 'yan bindiga

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da bayar da umarnin a gaggauta biyan hakkokinsu

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar cewa wasu jami'anta guda 7 sun rasa ransu yayin da aka garzaya da wasu 11 zuwa asibiti sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa dasu a hanyarsu ta zuwa Katsina.

A cikin jerin wasu takaitattun sakonni da rundunar 'yan sanda ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewa hatsarin ya ritsa da 'yan sandan yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Katsina domin gudanar da aiki.

Babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), M. A Adamu, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan jami'an da suka mutu.

Kazalika, ya bayar da umarni a gaggauta biyan hakkokinsu tare da sanar da cewa rundunar 'yan ssanda za ta dauki nauyin jinyar sauran jami'ai 11 da ke kwance a asibiti.

Jami'an 'yandan na sashen SFU (Special Forces Unit) sun gamu da hatsarin mota a kan hanyar Zaria zuwa Kaduna yayin da su ke tafiya zuwa jihar Katsina a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli.

Jami'an 'yan sanda 7 sun rasa ransu a jihar Katsina
Jami'an 'yan sanda
Asali: UGC

An tura jami'an ne domin kara tsananta yakin da rundunar 'yan sanda ke yi domin dakile aiyukan 'yan bindiga a yankin karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna da sauran wasu sassan jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Ma su garkuwa da mutane sun sace tsohon sanatan arewa har gida

Hatsarin, wanda ya ritsa da motar jami'an 'yan sanda kirar 'Hummer Bus' mai cin mutum 18, ya afku ne a daidai garin Jaji a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Da ya ke bayyana mutuwar 'yan sandan a matsayin babban rashi ga rundunar 'yan sanda, IGP ya ce jami'an da su ka mutu sun shiga cikin jerin ''jaruman zaman lafiya''.

A karshe, ya yi mu su addu'ar samun jin kai a wurin Ubnagiji tare da bawa iyalinsu hakurin jure rashinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel