Matar aure ta kashe aurenta bayan cewa da tayi za ta iya cin amanar mijinta a kan N200,000

Matar aure ta kashe aurenta bayan cewa da tayi za ta iya cin amanar mijinta a kan N200,000

- Kamar yadda wani ma'abocin amfani da Twitter Gospel Josiah ya wallafa, matar ta tabbatar da cewa za ta iya cin amanarta mijinta a kan N200,000

- Ta sanar da hakan a matsayin martanin ta ga wata tambaya da aka yi mai cewa ko za a iya cin amanar abokin rayuwa a kan N10 miliyan

- Tsokacin daga bisani ya isa kunnen mahaifiyar mijinta kuma hakan yasa aka tsinke igiyar aurenta duk da ta yi nadama

Wani ma'abocin amfani da Twitter ya bai wa mutane mamaki bayan da ya wallafa labarin yadda wata mata ta kashe aurenta a kan wani tsokaci da tayi a Facebook.

Kamar yadda labarin ya bayyana, an tambaya 'yan kungiyar ko za a iya cin amanar abokin rayuwa a kan N10 miliyan.

Matar da ba a dade da yin aurensu ba, ta ce wannan makuden kudin sun yi mata yawa. Za ta iya cin amanar mijinta matukar za a biya ta N200,000 kacal.

Wannan tsokacin kuwa ya kawo karshen auren matar don mutane masu tarin yawa sun gani.

"Ta ce wannan kudin ya yi mata yawa da har za ta ci amanar mijinta. Idan aka bata N200,000 kadai ta isheta. Wani da ya santa ya bukaci ta goge tsokacinta saboda an daura mata aure," Josiah ya wallafa.

KU KARANTA: Rahoton siya wa da gidan N300m: Malami ya yi barazanar maka wata jarida a kotu

Kamar yadda ci gaban labarin ya bayyana, wasu mutum biyu sun bukaci ta goge tsokacin amma sai ta hada musu da tsageranci tare da kin gogewa.

Daga bisani ta goge tsokacin amma wani dan uwan mijinta ya riga ya dauka hoton shi kuma ya tura wa uwar mijinta wacce babbar ma'aikaciyar gwamnati ce kuma babba a cocinsu.

Wannan lamarin ya kawo hargitsi don kuwa tuni aka kira taron 'yan uwa don shawo kan matsalar.

An kira matar inda ta bayyana tana kuka tare da cewa wasa take yi amma 'yan uwan mijin suka ki karbar ban hakurinta.

Kamar yadda Josiah ya sanar, tuni aka warware auren kuma aka bukaci mijin da ya karba sadakinsa da ya bada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel