Jami'an tsaro sun garkame ofishin Magu

Jami'an tsaro sun garkame ofishin Magu

- Kwamitin fadar shugaban kasa na ci gaba da bincikar dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu

- A yanzu haka an tattaro cewa an kwace wasu motoci biyu na ofishin dakataccen shugaban EFCC din

- Har ila yau jami'an tsaro sun kai samame ofishinsa inda suka garkame ofis din

A jiya Litinin, 13 ga watan Yuli, an ci gaba da bincikar dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a gaban kwamitin fadar shugaban kasa.

An zargesa da yin amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba tare da damfara.

Bayan komawar binciken kwamitin, manyan jami'an hukumar da daraktoci sun hallara gaban kwamitin inda suka ci gaba da bayani.

A cikin binciken, an kwace wasu motoci biyu na ofishin dakataccen shugaban EFCC.

An samo daya a Abuja inda dayar aka samota daga Maiduguri. An ajiye su a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Jami'an tsaro sun garkame ofishin Magu
Jami'an tsaro sun garkame ofishin Magu Hoto: The Cable
Asali: UGC

Daily Sun ta tattaro cewa har ila yau kwamitin na tuhumar Magu a kan kudaden atisaye a kasar waje na shekaru uku.

Koda dai ba a gudanar da atisayen ba, an tattaro cewa kwamitin ya gabatar da tuhuma game da kasafin shirye-shiryen.

An tattaro cewa hukumar, a shekaru uku da suka gabata, tana ware naira miliyan 700 duk shekara, na atisayen jami’ai da ma’aikata a kasar waje.

Sai dai kuma an tattaro cewa babu wani ma’aikaci da aka taba turawa waje domin wani horo kuma an kasa bayar da bayani na kasafin naira biliyan 2.1 da aka ware a shekaru uku.

Daraktoci da sauran jami’an hukumar ma sun amsa tambayoyi.

An sake ganowa cewa, jami'an FCID sun rufe ofishin Magu da ke hawa na tara a sabbbin ofisoshin EFCC da ke Jabi a Abuja.

Jami'an sun kara da rufe ofishin sa da ke Wuse II. An hana hadimansa shiga ofisoshin ko ginin da ofisoshin suke.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Okowa da matarsa sun warke daga cutar COVID-19

Majiyar ta tabbatar da cewa jami'an sun isa inda ofishin yake tare da garkame shi ba tare da yin wani bayani ga sauran jami'an hukumar da suka tsaya suna kallo cike da mamaki ba.

"A yau sun zo sun rufe ofishin. Sun hana hadiman da ke masa aiki da wadanda ke kusa da wurin shiga ofisoshinsu. Wasu sun tafi gida yayin da wasu suka dinga yawo suna kallo."

A baya mun ji cewa an lalube ofishin Ibrahim Magu ne a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami ya ke yi a kan tsohon shugaban hukumar na EFCC.

Rahotan ya fahimci cewa an dauki wata na’ura mai kwakwalwa daga ofishin shugaban hukumar. Ana tunanin za a samu muhimman bayanai a cikin wannan gafaka.

Bayan haka kuma masu binciken sun taso wasu manyan jami’an EFCC a gaba da tambayoyi jiya Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel