Yadda kwamitin bincike ya taso keyar wasu manyan Jami’an Hukumar EFCC

Yadda kwamitin bincike ya taso keyar wasu manyan Jami’an Hukumar EFCC

Kwamitin shugaban kasa da ke binciken zargin da ke kan tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya na cigaba da kokarin bankado ta’adin da aka yi a hukumar.

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, jami’an tsaro su ka shiga ofishin Ibrahim Magu, su ka yi binciken kurilla, su ka tafi da na’ura, kuma a karshe su ka rufe ofishin.

Jaridar Vanguard ta ce a wannan rana ta jiya, an gayyaci wasu manyan jami’an hukumar EFCC su amsa tambayoyi game da binciken da ake yi.

Rahoton da mu ka samu ya bayyana cewa jami’ai akalla uku ne su ka bayyana a fadar shugaban kasa a gaban kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

Daga cikin wadanda lambarsu ta fito har da Mohammed Umar wanda ya kasance darektan gudanarwa a lokacin da Magu ya ke rike da shugabancin hukumar.

Ibrahim Magu ne ya kawo Mohammed Umar cikin hukumar EFCC. Umar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne shekaru hudu da su ka wuce.

KU KARANTA: An turo wasu Jami’an tsaro sun yi wa ofishin Ibrahim Magu ta-tas a EFCC

Yadda kwamitin bincike ya taso keyar wasu manyan Jami’an Hukumar EFCC
Shugaban Hukumar EFCC da aka dakatar
Asali: UGC

Bayan an dakatar da Magu a makon da ya gabata, ministan shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana Umar a matsayin shugaban rikon da zai jagoranci ragamar EFCC.

Wani ma’aikacin EFCC ya shaidawa jaridar Vanguard: “Jami’an EFCC uku aka gayyata domin ayi masa tambayoyi a gaban jami’an tsaro.”

Ya ce: “An ajiye su ne a wurare daban da juna, kuma ba a ba su damar ganawa da Magu ba.”

“Kwamitin sun dura ofishin EFCC tsakanin karfe 12:00 zuwa 2:00 na rana, sannan su ka tafi da Osas da Buhari (jami’in EFCC ba shugaban kasa ba).”

Majiyar ya ce: “Ba zan iya tuna na ukunsu ba. Har zuwa karfe 8:40 na dare, dukkansu har da Magu su na gaban kwamitin a tsohon dakin taron fadar shugaban kasa a Abuja.

Kawo yanzu ba mu da masaniya game da yadda binciken ya ke gudana a fadar shugaban kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel