Gwamna Okowa da matarsa sun warke daga cutar COVID-19
- Matar gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ta warke daga cutar korona da ta kama ta
- Uwargidar gwamnan da diyarta sun kamu da cutar korona a yan kwanakin da suka gabata
- Gwamnan ya bayyana warakar matarsa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli
Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, matarsa da diyarsa da suka kamu da cutar korona duk sun warke.
Ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.
"Mata ta, diyata da ni kaina duk mun warke daga cutar korona. Ba mu kadai ba, har da sauran iyalina da suka kamu da muguwar cutar.
"Muna godiya ga Ubangiji kuma muna mika sakon godiya ga duk wadanda suka taimaka mana da addu'a," ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Gwamnan Okowa yayi wannan sanarwar ne a sahihin shafinsa na Twitter.
Ya sanar da lokacin da suka kamu da muguwar cutar tare da bayyana cewa sun killace kansu.
Hakan ya faru ne bayan daya daga cikin 'ya'yan shi mata ta harbu da muguwar cutar numfashin.
KU KARANTA KUMA: Dangantaka ta da Buhari tamkar na uba da ‘da ne - Obaseki
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 595 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.40 na daren ranar Litinin 13 ga Yulin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 595 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-156
Oyo-141 FCT-99
Edo-47
Kaduna-27
Ondo-22
Rivers-20
Osun-17
Imo-13
Plateau-10
Nasarawa-8
Anambra-8
Kano-5
Benue-5
Borno-5
Ogun-4
Taraba-3
Gombe-3
Kebbi-1
Cross Rivers-1
Jimillan wadanda suka kanu 33,153
Wadanda suka warke 13,671
Wadanda suka mutu 744
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng