Babu yadda Magu zai iya awon gaba da kudin da EFCC ta karbe – inji Lauyansa

Babu yadda Magu zai iya awon gaba da kudin da EFCC ta karbe – inji Lauyansa

- Lauyan Ibrahim Magu ya ce wanda su ke karewa bai aikata wani ba daidai ba

- Sai dai har yanzu Lauyoyin Magu ba su san laifin da ake tuhumar shi da su ba

- Wahab Shittu ya ce duk da haka a shirya su ke su wanke Magu a gaban Alkali

Wahab Shittu wanda Lauya ne na shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, wanda kuma ya ke tsare tun a farkon makon jiya, ya yi magana game da binciken da ake yi.

Wannan babban Lauya ya yi hira da jaridar Daily Trust, inda ya karyata zargin da ake yi wa Ibrahim Magu na satar kudin sata, da sauransu.

Barista Wahab Shittu ya ce babu yadda za ayi Magu ya sace kudin da ya karbo daga hannun barayi.

Kamar yadda ku ka samu labari, Lauyan ya bayyana cewa Naira biliyan 550 din da hukumar EFCC ta yi nasarar karbewa ba su kawo ruwa a banki.

Shararren lauyan ya yi karin haske da cewa muddin kudi su ka shiga cikin asusun TSA a babban bankin Najeriya, ba za su iya samar da ruwa na ajiya ba.

A game da batun karbar beli, lauyan ya ce Magu bai da niyyar kalubalantar gwamnatin tarayya ko shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma zai jira gaskiya ta yi aiki.

KU KARANTA: Bincike: An shiga ofishin Magu, an tsare Mukarrabansa da tambayoyi

Babu yadda Magu zai iya awon gaba da kudin da EFCC ta karbe – inji Lauyansa
Ibrahim Magu da DG NYSC
Asali: UGC

“Magu ya na ganin girman shugaban kasa, kuma ya yarda shugaban kasar zai duba lamarinsa da adalci da gaskiya domin a na sa hangen, Magu bai da laifi, kuma akwai takardun da za su fito da gaskiyarsa.”

Shittu ya ce: “(Magu) Zai jira, gwamnati ta san cewa babu dalilin cigaba da tsare shi, rufe shi ba shi da wani amfani. Ba haka za a saka masa da irin bautar da ya yi wa kasa ba.”

“Ina so jama’a su sani cewa tun da aka kafa hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi nasarar da babu wani shugaban da ya samu a bangaren gurfanarwa, da karbo dukiyar sata.”

“A shirya mu ke 100-bisa-100 mu kare Magu a gaban kuliya. Abin da mu ke bukata shi ne a ba mu jerin laifuffukan da ake zargin shugaban hukumar da aikatawa.” inji sa.

Lauyan ya ke amsa tambaya a kan shirinsu na nemawa tsohon shugaban na EFCC gaskiya a kotu.

Idan ana tuhumar ka da laifi, ka na da damar a baka takardar da ke kunshe da zargin da ke kan ka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel