Jami’an tsaro sun dauki gafaka bayan sun binciki ofishin tsohon Shugaban EFCC Magu

Jami’an tsaro sun dauki gafaka bayan sun binciki ofishin tsohon Shugaban EFCC Magu

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, aka tura wasu masu bincike da su ka su ka tsefe ofishin shugaban hukumar EFCC da aka dakatar watau Ibrahim Magu.

Jaridar The Nation ta ce an lalube ofishin Ibrahim Magu ne a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami ya ke yi a kan tsohon shugaban hukumar na EFCC.

Rahotan ya fahimci cewa an dauki wata na’ura mai kwakwalwa daga ofishin shugaban hukumar. Ana tunanin za a samu muhimman bayanai a cikin wannan gafaka.

Bayan haka kuma masu binciken sun taso wasu manyan jami’an EFCC a gaba da tambayoyi jiya.

Majiyar hukumar ta fadawa jaridar cewa: “Masu binciken sun lalube ofishin, sannan su ka tafi da wata babbar gafaka da ake zargin akwai bayanai a cikinta.”

“An bukaci wasu manyan mukarraban Magu su bayyana a gaban kwamitin binciken domin su yi wasu karin bayani. Su na wurin har kusan karfe 9:30 na dare.”

KU KARANTA: Faston da ake zargin ya hada-kai da Magu wajen satar kudi ya yi magana

Jami’an tsaro sun dauki gafaka bayan sun binciki ofishin tsohon Shugaban EFCC Magu
Shugaban kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu
Asali: UGC

Bayan an laluba ofishin na Magu, an kuma tsare wasu manyan hadimansa. Jaridar ta The Nation ta ce an yi wa mukarraban tsohon shugaban hukumar tambayoyi a jiya.

Daga cikin wadanda aka rutsa a binciken akwai wani mukaddashin darektan harkokin karbe dukiyar sata na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon-kasa.

An karbe wayoyin wasu daga cikin wadannan hadimai inda aka binciki wasu bayanai. A karshe an kyale su sun tafi gida bayan dare ya tsala.

Ana tunanin cewa kwamitin ya na neman karin bayani ne a game da wasu kadarori 332 da hukumar EFCC ta karbe daga hannun barayi a karkashin Ibrahim Magu.

Majiyar ta ce: “Ina tunanin cewa an bukaci ganin Aliyu Yusuf ne a game da wasu kadarori da aka karbe daga hannun wadanda ake tuhuma da satar dukiyar gwamnati.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel