APC ta gaza shawo kan Gwamna Fayemi da Abokan fadarsa a jihar Ekiti

APC ta gaza shawo kan Gwamna Fayemi da Abokan fadarsa a jihar Ekiti

- Har yanzu ba a kawo karshen bambancin da aka samu a gidan APC a jihar Ekiti ba

- Ba a ga maciji tsakanin magoya bayan Gwamna Kayode Fayemi da ‘yan adawarsa

- Jiga-jigan Jam’iyyar APC su na ta faman kai wa juna hari tun lokacin zaben 2018

Jaridar The Punch ta fitar da wani dogon rahoto da ya bayyana cewa sabanin da aka samu a jam’iyyar APC a jihar Ekiti tun lokacin zaben 2018 ya na kara bayyana baro-baro.

Ana samun hakan ne bayan bambancin da ke tsakanin magoya bayan gwamna mai-ci Dr Kayode Fayemi da wani daga cikin manyan abokan hamayyarsa ya na kara fitowa.

Wadanda su ka kara da Fayemi wajen samun tikiti a APC a 2018 sun hada da irinsu Segun Oni; Sanata Babafemi Ojudu; Dr. Oluwole Oluyede; Bimbo Daramola; Oyetunde Ojo da sauransu.

Bayan irinsu Muyiwa Olumilua, Dr Mojisola Yaya-Kolade da Bamidele Faparusi, mafi yawan manyan ‘yan siyasar APC ba su hada-kai da Fayemi bayan ya kafa gwamnati ba.

Hadimin shugaban kasa, Femi Ojudu, wanda ya janyewa Fayemi takara ana shirin zabe ba ya tare da gwamnan har gobe. Shi kuwa Segun Oni tuni ya koma PDP bayan dakatar da shi a APC.

Segun Oni ya rika kukan ba a iya masa da mutanensa adalci a APC. Shugaban APC na jihar Ekiti, Paul Omotoso, ya maidawa Segun Oni martani, ya ce kwadayin mulki ya ke yi.

KU KARANTA: Mutane 9 da ke harin kujerar Gwamna Akeredolu a jam'iyyar APC

APC ta gaza shawo kan Gwamna Fayemi da Abokan fadarsa a jihar Ekiti
Mai girma Gwamna Kayode Fayemi
Asali: Depositphotos

Akwai wasu manyan ‘yan APC 15 da ba su ga maciji da gwamna Fayemi, Jagoran wannan tawaga shi ne Sanata Ojudu wanda mai bada shawara ne a fadar shugaban kasa.

Sauran fusatattun ‘yan APC a jihar su ne: Sanata Adedayo Adeyeye; Sanata Tony Adeniyi; Hon. Oyetunde Ojo, Daramola, da Robinson Ajiboye. Ragowar sun hada da Adewale Omirin.

Wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya sun zargi gwamna Fayemi da korar duk wadanda su ka ja da shi daga jam'iyyar ta APC mai mulki a jihar.

Su ka ce daga cikin wadanda aka kora ko ake shirin kora a APC a Ekiti akwai Adeniyi, Ojudu, Daramola, Ojo, Akogun Bunmi Ogunleye, Ben Oguntuase, Dele Afolabi da Diran Fadipe.

Dattawan jihar Ekiti sun fara kira ga wadannan ‘yan siyasa su ajiye kayan yakinsu, su hada-kai da gwamnati domin ganin jihar Ekiti ta cigaba.

Shugaban sarakunan Ekiti, Alawe na kasar Ilawe, Oba Adebanji Alabi ya yi tir da rikicin da ake yi. Tsohon mataimakin gwamnan jihar Abiodun Aluko, ya yi irin wannan kira.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng