Gwamna El-Rufai ya ce kishin Keyamo ya sa Shugaban kasa ya ke ji da shi

Gwamna El-Rufai ya ce kishin Keyamo ya sa Shugaban kasa ya ke ji da shi

- Gwamnan Kaduna ya bayyana alakar da ke tsakanin Festus Keyamo da Shugaban kasa

- Nasir El-Rufai ya ce tsantsagwaron kishin Ministan kasar ya jawo masa kaunar Buhari

- Ana rikici da Ministan a game da wasu ayyuka da za a rabawa matasa 774, 000 a kasar

Kwanakin baya aka yi ta samun matsala tsakanin majalisar tarayya da karamin ministan ayyukan kwadago da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo.

A dalilin wannan takkadama da aka samu tsakanin manyan kasar, wani ‘dan jarida Desmond Ike-Chima ya yi wani rubutu ya na yabon ministan tarayyar.

Festus Keyamo SAN ya ji dadin wannan rubutu da editan gidan jaridar Myemag.net ya yi, har ya wallafa rubutun a kan shafinsa na Twitter.

Bayan nan ne gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya yi magana game da ministan, ya ba shi shawarar cewa ya tsaya tsayin daka a jajircewar da aka san sa da shi.

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yabi Keyamo, wanda ya kira mutumin kwarai kuma mai kishi.

KU KARANTA: Minista ya karyata zargin fasa bututun man Neja-Delta

Gwamna El-Rufai ya ce kishin Keyamo ya sa Shugaban kasa ya ke ji da shi
Festus Keyamo
Asali: UGC

“Minista Festus Keyamo @fkeyamo ‘dan kishin kasa ne mai jajircewa. Mutumin kirki ne wanda manufofinsa da ayyukansa su ke kan kare al’umma da marasa gata.”

Mai girma Gwamnan na jihar Kaduna ya kara da cewa: “Wannan ne ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke kaunarsa kamar ‘dansa.”

Malam Nasir El-Rufai ya kara da ba ministan shawara: “Ka tsaya tsayin daka ‘danuwana.”

Wannan magana da gwamna Nasir El-Rufai ya yi a ranar Lahadi a kan shafinsa na Twitter ta yi farin-jini, mutane kusan 3, 000 su ka nuna cewa sakon ya burge su.

Jim kadan bayan nan sai Keyamo ya maidawa tsohon ministan na babban birnin tarayya martani, ya na godiya da wannan goyon baya da shawara mai muhimmannci.

“Nagode ran ka ya dade. Lallai wannan ya kara mani kwarin gwiwa.”- Festus Keyamo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng