Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa

Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa

Ibrahim Magu, dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC), ya ce babu gaskiya a zargin da ake masa na sake wabtare kudaden da ya karbo daga mahandama.

Kwamitin bayani a kan handamammun kudin na fadar shugaban kasa (PCARA) ya zargi Magu da sake kwashe dukiyar da aka kwato daga mahandama.

Kwamitin na bincikar kadarorin da EFCC ta samo tun daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2020.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana, kwamitin fadar shugaban kasar sun zargi Magu da kwashe ribar saman kudi N550 biliyan da aka samo a kasar nan.

Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa
Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Amma kuma, Wahab Shittu, lauyan Magu, ya bayyana hakan a matsayin ikirarin da ba gaskiya ba.

Yace kudaden da aka samo an zuba su ne a asusu bai daya na gwamnati wato TSA a babban bankin Najeriya, ya kara da cewa irin wannan asusun baya kawo riba a kan kudi.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda

"Karya ne idan aka ce Magu ya saka kudin a asusun bankin da ke kawo riba," jawabin yace.

"Wannan zargin bai bayyana ba a gaban kwamitin fadar shugaban kasar karkashin Salami. Basu tunkari Magu da wannan zargin ba, masu yada labarai ne ke ta wallafawa.

"A abinda Magu ya sani, babu irin wannan kudin a irin asusun nan. Babu wanda ya tunkari Magu da wannan zargin.

"Dukkan kudin da aka samo ana zuba su ne a asusu mai tsarin TSA a babban bankin Najeriya. A don haka ba a samun riba a kan kudin. Wannan bayyananne ne kuma CBN da ma'aikatar kudi za su iya fayyace hakan.

"Sauran ma'aikatun gwamnati za su iya shaidar hakan don kudi a TSA basu janyo riba."

An kama Magu a ranar 6 ga watan Yuli. Yana fuskantar tuhuma daga kwamitin fadar shugaban kasa karkashin shugabancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara.

A gefe guda, Malamin addinin kirista, Emmanuel Omale ya yi magana game da zarginsa da ake yi da hannu wajen sayen wani gida na Naira miliyan 573 da sunan Ibrahim Magu.

Emmanuel Omale ya karyata wannan zargi, ya kuma ce zai iya kai kara gaban kotu ta bakin Lauyansa, Gordy Uche (SAN), ya nemi a biya shi Naira biliyan daya na bata masa suna da aka yi.

Faston ya ce babu shakka ya hadu da Ibrahim Magu kwanakin baya a birnin Dubai a shekarar nan, amma ya ce sam ba batun sayen gida ta hada su ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng