Gwamnatin Obasanjo ta dasa matsalar da ake fuskanta a EFCC – Ishola Williams

Gwamnatin Obasanjo ta dasa matsalar da ake fuskanta a EFCC – Ishola Williams

Ishola Williams mai ritaya wanda fitaccen soja ne wanda ya rike mukami da –dama, kuma aka san shi da tsayin daka, ya yi magana game da rikicin da ake samu a hukumar EFCC.

Janar Ishola Williams ya yi hira da jaridar Vanguard a karshen makon nan inda ya bayyana ra’ayinsa game da abin da ya kai har ake samun matsala da Ibrahim Magu a EFCC.

“Dakatar da Magu da bincikensa da ake yi ya burge ni domin mutane sun dade su na so su nan wanene ke binciken wadanda su ke yin bincike. Babu wanda ya ke da tabbacin wa ke lura da hukumomin yaki da rashin gaskiya." inji Williams.

Mutane su na ganin cewa fadar shugaban kasa ce kurum ke da ikon cewa ga wanda za a tuhuma, ko kuma wanda za a kyale a Najeriya inji tsohon sojan.

Williams wanda ya rike babban jami’i na Transparency International a Najeriya ya ke cewa: “Babu shakka akwai matsala tsakanin AGF da mukaddashin shugaban EFCC da aka dakatar.”

“Ina tunanin Magu ya raina wasu abubuwa ne, ya na tunanin cewa AGF bai isa ya tsige shi daga ofis ba, ya dauka shugaban kasa kurum zai iya tsige shi. Haka ne, amma ya manta cewa AGF shi ne mai ba shugaban kasa shawarar shari’a.”

KU KARANTA: Magu ya yi waje, Umar ya hau kujerar EFCC

Gwamnatin Obasanjo ta dasa matsalar da ake fuskanta a EFCC – Ishola Williams
Abubakar Malami da Buhari
Asali: Depositphotos

Janar Williams ya ce bai yarda Magu lauya ba ne, kuma zai so yaji labarin makarantar da ya yi karatu da kuma malamansa. A cewarsa, Magu ya manta cewa ministan shari'a ya fi karfinsa.

Bayan raina Minista da shugaban na EFCC ya yi, Williams ya na ganin cewa gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo ta jawo matsalar da ake fama da ita a EFCC tun farko wajen kafa ta.

Ba wannan ba ne karon farko da ake rikici da shugaban EFCC kafin su bar ofis, an yi da Nuhu Ribadu, Farida Waziri, da Ibrahim Lamorde, Janar din ya ce ainihi akwar matsala a tsarin hukumar.

“Tsarin shugabancin hukumar EFCC ya kawo wata mummunar al’ada, idan ka na da hukuma, dole ka raba ta da shugabanninta. Kowace hukuma ta na da shugabannin da ke lura da ita.”

"EFCC ne kurum shugabanninsu su ke tare da majalisar da ke lura da su. Wannan ya sa shugabannin ICPC da EFCC za su iya yin abin da su ka ga dama, babu mai lura da su, sai shugaban kasa.”

“Wannan laifin Obasanjo ne, shi ya yi wannan aikin a lokacin da ya ke mulki. Da gan-gan ya yi haka saboda bai son wani ya sa masa ido.” A cewar Janar Ishola Williams.

Ya ce don haka ya zama cewa babu wanda ya isa da Ribadu duk da cewa DCP ne shi a gidan ‘yan sanda. Irin wannan abu ne ya faru da Magu wanda yanzu ake tuhuma da zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel