Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti

Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti

Shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma masu yiwa dukiyar al'umma zagon kasa, Ibrahim Magu da aka kora, ya isa fadar shugaban kasa a ci gaba da tuhumarsa da ake yi kan aikata laifukan almundahana.

Magu ya isa tsohon babban dakin taro na fadar shugaban kasar da ke Abuja, wurin da aka kebe don gudanar da tuhumar, da misalin karfe 9:00 na safe.

A makon da ya gabata, wasu daga cikin jami'an hukumar EFCC sun gurfana gaban kwamitin binciken karkashin mai shari'a Ayo Salami.

Haka zalika ana saran wasu daga cikin jami'an hukumar su sake bayyana gaban kwamitin a yau Litinin, yayin da aka umurci wasu daraktoci da shuwagabanni sashe sashe dasu sake bayyana gaban kwamitin a ranar Talata dauke da wasu muhimman takardu.

KARANTA WANNAN: Dasuki ya magantu a kan zargin hada baki da Buhari lokacin da ya ke tare da Jonathan

A ranar Juma'ar da ta gabatan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar dakatar da Magu daga mukamin mukaddashin shugaban hukumar EFCC, inda kuma amince da nadin daraktan gudanar da ayyuka na hukumar, Mohammed Umar, a matsayin wanda zai ci gaba da jan ragamar hukumar har zuwa lokacin da kwamitin da fadar shugaban kasar ta kafa zai kammala bincike.

Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti
Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti
Asali: UGC

Babban alkalin alkalai na kasa kuma ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a ranar Juma'a.

A cewar sanarwar da ta fito daga hannun hadimin Malami ta fuskar watsa labarai, Dr Umar Gwandu, shugaban kasar ya amince da dakatarwar ne "domin baiwa kwamitin binciken da fadar shugaban kasar ta kafa damar gudanar da bincikenta ba tare da wani tsaiko ba."

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasa Buhari ya amince Umar ya ci gaba da jan ragamar ayyukan hukumar har zuwa lokacin da za a kammala wannan bincike.

A wani labarin makamancin wannan, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, shahararren lauyan nan na Nigeria kuma mai kare hakkin bil'Adama, Femi Falana (SAN) ya baiwa jaridar The Nation wa'adin awanni 48 da ta rubuta masa wasikar ban hakuri, tana mai amincewa da cewar labarin da ta wallafa a shafinta na farko akansa karya ne tsagoronta.

Falana ya bayar da wannan wa'adin ne ta hannun CITIPOINT, wani ofishin lauyoyi da ke da zama a Lagos. Barazanar wacce ke a cikin shafuka uku ta hakaito taken labarin da jaridar ta wallafa da, "Magu na fuskantar wani babban kalubale yayin da sabbin alkaluma suka sake bayyana kan kudaden satar da aka kwato.

Jaridar ta wallafa labarin a ranar 12 ga watan Yuli, 2020, a inda kafar watsa labaran ta alakanta Femi Falana da Naira miliyan 28 daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya handame.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng