Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda

Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda

An zargi dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, da mayar da EFCC tamkar ofishin 'yan sanda saboda wani ra'ayi nashi na kanshi.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar, wannan na kunshe ne a rahoton kwamitin kula da yadda aka samo dukiyoyin da aka handame na fadar shugaban kasa (PCARA).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin don ya duba al'amuran EFCC karkashin jagorancin Magu.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, "Nuna tunkaho tare da tara dukiya ba ta hanyar halal ba ya mayar da EFCC tamkar wani babban ofishin 'yan sanda," yace.

Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda
Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Duk da diban ma'aikatan da aka dinga yi a hukumar a shekarun da suka gabata, Magu yana tattara 'yan sanda a hukumar don ya fi jin dadin yin rashin gaskiyarsa tare da 'yan sanda.

"Ya fi aiki da 'yan sandan duk da jami'an EFCC sun fi su kwarewa wurin bincike a kan tattalin arziki da laifukan da suka shafi kudi."

A ranar Juma'a da ta gabata ne sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bada umarnin janye 'yan sandan da ke tsaron lafiyar Magu wanda aka tsare.

A halin yanzu, kwamitin fadar shugaban kasa ke bincikarsa karkashin jagorancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara.

Ana zargin sa da kumbuya-kumbuya wurin bayyana adadin dukiyar da aka samo daga mahandama.

A ranar Litinin da ta gabata ne jami'an DSS da na FCID suka kama Magu.

A baya mun ji cewa ana zargin Ibrahhim Magu, da kin bayar da cikakken bayani kan kadarori 332 da suka bata cikin 836 da aka kwato a watan Maris, 2018.

Wani rahoto daga kwamitin bayani a kan kudaden da aka samo (PCARA) ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kasa ta bada bayanin wasu kadarorin biliyoyin naira.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya sanar, rahoton ya ce an samu asara da tagayyarar kadarori, motoci da sauran su duk da aka samo daga mahandama.

Ya kara da nuna damuwarsa kan yadda aka kasa adana dukiyoyin da gane darajarsu ta fuskacin tattalin arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel