EFCC: Yadda aka kare da tuhumar masu tuhuma 4 da suka taba shugabancin EFCC

EFCC: Yadda aka kare da tuhumar masu tuhuma 4 da suka taba shugabancin EFCC

Alamu masu yawa na nuna cewa shugabancin hukumar yaki da rashawa ta EFCC na karewa a hagungunce.

Babu shugaban hukumar daya da zai ce ya bar kujerarsa cike da salama tun bayan kafa hukumar da aka yi a 2003.

Dukkaninsu sukan kare a wani hali na daban a yayin da suke yakar rashawa.

Abinda ke faruwa a halin yanzu da Magu ba komai bane face bin sahun wadanda ya gada.

EFCC: Yadda aka kare da tuhumar masu tuhuma 4 da suka taba shugabancin EFCC
EFCC: Yadda aka kare da tuhumar masu tuhuma 4 da suka taba shugabancin EFCC Hoto: The Cable
Asali: UGC

Tun da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kirkiri hukumar, babu wanda ya shugabanci hukumar da kwazo fiye da Malam Nuhu Ribadu.

Dan sandan wanda ya samu damar yakar rashawa yayi suna babu jimawa a fadin kasar nan. Da kanshi ya dinga durkusar da manyan 'yan siyasa.

A karkashin shugabancin sa, ya firgita 'yan siyasa masu handama amma babu jimawa aka san yadda aka yi har ya bar ofishin.

Bayan horarwar shekara daya da aka umarcesa da ya yi, an sallamesa daga aiki cikin ruwan sanyi.

Farida Waziri ce ta maye gurbinsa inda ta karbi ragamar mulkin hukumar.

Kafin a tabbatar da ita, ta musanta zargin da ake mata na tsayawa tsohon gwamnan Benue, George Akume a yayin da ake zargin sa da wabtar kudi.

Babbar nasararta shine yadda ta bibiyi damfarar da Bode George yayi. Bayan rasuwar 'Yar'adua ne tayi kaurin suna.

Hawan Goodluck Jonathan mulkin Najeriya yasa aka sallameta.

Bayan saukar Farida Waziri, Ibrahim Lamorde ya yi aiki a matsayin mukaddashin shugaban hukumar tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2008.

Bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban, ana kallonsa a matsayin kashin bayan binciken da duk Ribadu yayi. Ana tsammanin mahandama ba za su ji dadi ba a hannunsa.

Babu jimawa ya samu sabani da shugaban kasa bayan da aka zargesa da rashin bada bayani a kan wasu makuden kudade ballantana wadanda Tafa Balogun kwasa.

KU KARANTA KUMA: Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai

Lamorde ya musanta hakan amma majalisar dattawa ta bukaci abada damar kama shi saboda kin bayyana da yayi a gurin bincike. Daga bisani ya tsallake wannan al'amarin.

Mutum na karshe da ke cikin badakalar shugabancin hukumar ta EFCC a yanzu, shine Ibrahim Magu.

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar dashi sakamakon zarginsa da ake da sake hamdame wasu kudaden da aka wato daga mahamdama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel