An bayyana Bruno Fernandes a matsayin ‘Dan wasan BPL na watanni biyu a jere

An bayyana Bruno Fernandes a matsayin ‘Dan wasan BPL na watanni biyu a jere

A ranar Juma’a 10 ga watan Yuli, 2020, aka bayyana Bruno Fernandes a matsayin gwarzon ‘dan wasan watan Yuni da ya gabata.

‘Dan wasan na Manchester United shi ne ya lashe wannan kyauta watanni biyu da su ka wuce.

Da wannan nasarori masu bin juna da ‘dan wasa Bruno Fernandes ya samu, ya nan a nufin ya maimaita wani tarihi da Cristiano Ronaldo ya ajiye.

Tsohon ‘dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo shi kadai ne wanda ya taba zama gwarzon EPL na wata sau biyu a jere.

A halin yanzu Bruno Fernandes ya zama ‘dan wasa na biyu a tarihin Manchester United da ya bar wannan tarihi a sakamakon nasarorinsa a Mayu da Yuni.

A watan da ya gabata, Fernandes ya doke abokin wasansa Anthony Martial, da sauran ‘yan takara hudu wajen samun wannan kyauta.

KU KARANTA: Rade-radin Messi zai bar La - liga ya yi karfi a Sifen

An bayyana Bruno Fernandes a matsayin ‘Dan wasan BPL na watanni biyu a jere
Bruno Fernandes Hoto: BPL
Asali: Getty Images

Wadanda ‘dan wasan tsakiyar ya doke su ne Danny Ings (Southampton), Conor Coady da Raul Jimenez (Wolves) da kuma Allain Saint-Maximin (Newcastle United).

Haka zalika a watan Yuni, Bruno Fernandes ne ya samu kyautar wanda ya ci kwallon da ta fi kowace kyau sakamakon kwallon da ya zurawa Brighton.

“Lokacin da ‘dan wasan Manchester United ya ci kyautar gwarzon wata sau biyu a jere shi ne abokin Bruno, Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Nuwamba da Disamban 2006.”

Manchester United ta bayyana wannan a shafinta na yanar gizo.

Ana sa ran cewa sabon ‘dan wasan zai shiga cikin wadanda za a sake zaba a matsayin gwarzon wannan wata mai-ci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel