Ondo: APC ta yi watsi da takarar na hannun daman Tinubu

Ondo: APC ta yi watsi da takarar na hannun daman Tinubu

Kwamitin tantance ma su neman takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin inuwar jam'iyyar APC ya yi watsi da daya daga cikin mutane 12 da ke burin samun tikitin yin takara a jam'iyyar.

Duk da kwamitin, wanda Alhaji Tijani Tumsa ke jagoranta, bai bayyana sunan dan takarar da ya watsar ba, jaridar Daily Trust ta ce sunansa Segun Abraham kuma mai biyayya ne ga jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

A ranar Juma'a ne kwamitin Tumsa ya kammala tantance 'yan takarar jam'iyyar APC da ke burin fafatawa a zaben cikin gida domin fidda dan takara guda daya da zai rike kambun jam'iyyar a zaben da za a yi cikin watan Oktoba.

Alhaji Tumsa ya bayyana cewa sun tantance 'yan takara 12 ta hanyar duba takardun karatunsu da kuma sauraron bayanan da su ka gabatar, sannan ya kara da cewa dan takarar da aka watsar bai cika ka'idojin da jam'iyya ta saka ba.

"Mun fara tantance 'yan takarar tun kwanaki biyu da su ka gabata. Akwai jimillar 'yan takara 12 kuma dukkansu sun halarci wurin tantancewar, wanda hakan ya bamu damar kammala aikinmu cikin kwanaki biyu da mu ka ware.

"Mun zauna da kowanne dan takara, mun bawa kowannensu maki bayan sauraron bayanansa da duba takardun karatu, kwarewarsa ta aiki, ilimin sanin kundin tsarin mulki da na jam'iyyar APC da sauransu.

"Daga cikin mutane 12 da su ka sayi fom din takara kuma su ka halarci tantancewa, kwamitinmu ya ga cancantar 'yan takara 11 da za su fafata a zaben cikin gida domin fidda dan takara.

"Dan takara guda daya da kwamiti ya jingine takararsa zai iya daukaka hukuncin da mu ka yanke zuwa gaba, ya na da wannan damar.

"Ina mika sakon jinjina ga dukkan 'yan takara saboda sun bamu hadin kai wajen ganin mun kammala wannan tantancewa a kan lokaci.

Ondo: APC ta yi watsi da takarar na hannun daman Tinubu
Segun Abraham
Asali: Twitter

"Zan yi amfani da wannan dama wajen mika sakon godiya ga uwar jam'iyya wacce ta yaba da nagartarmu tare da ganin dacewarmu wajen gudanar da wannan muhimmin aiki," a cewar Tumsa.

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana illar da dakatar da zana WAEC za ta yi wa Najeriya

Da ya ke karbar rahoton kwamitin, sakataren kwamitin tsare - tsaren gudanar da zaben fidda 'yan takarar gwamnan Ondo a jam'iyyar APC, Sanata John Udoedehe, ya yabawa kwamitin Tumsa bisa kyakyawan aiki da ya yi.

Udoedehe ya bawa kwamitin Tumsa tabbacin cewa za su mika rahoton kammala tantance 'yan takarar zuwa kwamitin koli domin daukan mataki na gaba.

'Yan takara 12 da kwamitin ya tantance sune; Rotimi Akeredolu, Joseph Olusola Iji, Odimayo Okunjimi, Olayide Owolabi Adelaml mni, Issacs Duerimini Kekemeke, Olusola Oke Alex, da lfeoluwa Olusola Oyedele

Sauran sun hada da Olajumoke Olubusola Anifowoshe, Awodeyi Akinsehinwa Akinola Colinus, Olubukola Adetula, Dakta Abraham Olusegun Michael da Dakta Nathaniel Adojutelegan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel