Atiku ya bayyana illar da dakatar da zana WAEC za ta yi wa Najeriya

Atiku ya bayyana illar da dakatar da zana WAEC za ta yi wa Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na dakatar da rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandire (WAEC) ba zai haifar wa da kasa 'da mai ido' ba.

A cikin wani jawabi da ya fitar ta hannun ofishinsa na yada labarai, Atiku ya bayyana cewa ya san da akwai bukatar daukan matakan kare rayukan jama'a a wannan lokaci na annobar korona.

Atiku, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya ce matasa miliyan 1.5 ne su ka zana jarrabawar WAEC a shekarar 2019.

A cewar Atiku, hana matasan zana jarrabawar WAEC a wannan shekarar zai mayar dasu baya a tsakanin sauran sa'anninsu na sauran kasashen nahiyar Afrika ta yamma da ke rubuta jarrabawar.

"Bai daidai bane, saboda ma su zuba jari a tattalin arzikin kowacce kasa suna duba alkaluman matasa da sauran ma su ilimi a kasa kafin su saka kudinsu.

"Tuni Najeriya ta na baya a bangarorin cigaba da yawa da suka hada da; saka yara a makaranta da cin jarrabawa.

"Wannan mataki na dakatar da zana jarrabawar WAEC zai kara haifar da rudani tare da kara dagula harkokin ilimi da kullum ke kara tabarbarewa.

Atiku ya bayyana illar da dakatar da zana WAEC za ta yi wa Najeriya
Atiku
Asali: Twitter

"A maimakon a soke zana jarrabawar gaba daya, akwai hanyoyin da za a iya bi domin ganin dakile hauhawar yaduwar annobar korona.

"Za a iya amfani da gine -ginen gwamnati da su ka hada da filayen wasa, makarantun firamare, sinima da sauransu, wajen rarraba daliban da za su zana jarrabawar domin ganin ba a samu cunkuso ba.

DUBA WANNAN: 'Kisan girmamawa': Wani miji ya kashe matarsa ta hanyar jefeta da duwatsu

"Ko kuma gwamnatin tarayya ta hada kai da hukumar WAEC wajen tsara tambayoyi ma su yawa da dalibai daban - daban za su ke rubutawa a mabanbantan lokuta, idan ya so sai a raba dalibai zuwa rukuni - rukuni tare da ba su lokutan zana jarrabawa.

"Hakan zai bawa gwamnati damar cin riba biyu; sa ido wajen tabbatar da dokar nesanta sannan kuma dalibai za su zana jarrabawarsu.

"Ina rokon wannan gwamnati ta sake duba halin da za ta jefa rayuwar matasan da ta ke ikirarin karewa, saboda matukar ba a janye wannan hukunci ba, dalibai da dama za su karya dokar nesanta ta hanyar tsallakawa zuwa kasashen ketare domin zana jarrabawar WAEC," a cewar Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce daliban Najeriya ba za su so yin asarar shekarar guda ba, hakan kuma zai sa da yawa daga cikinsu yanke shawarar tsallakawa makwabtan kasashe domin su rubuta jarrabawar WAEC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel