'Kisan girmamawa': Wani miji ya kashe matarsa ta hanyar jefeta da duwatsu
Ana zargin wani magidanci tare da dan uwansa da jefe matarsa mai shekaru 24 bisa tsarin al'adar kasar Pakistan ta 'kisan girmamawa'.
An tsinci gawar matar kaca - kaca da raunuka a gefen wata babbar hanya da ke daura da Indus mai makwabtaka da kauyen Wadda Chacha a kasar Pakistan a ranar 27 ga watan Yuni.
Kisan girmamawa, wanda a kan mata kadai ake zartar da shi, wata bahaguwar al'adace da ta bawa miji ko dangin mace damar kasheta saboda ta aikata wani abin kunya.
An kashe matar, wacce kafafen yada labarai na kasashen ketare su ka bayyana sunanta da 'Waziran', a birnin Jamshoro da ke gundumar Sindh a kasar Pakistan, kamar yadda jaridar 'The Mirror' ta rawaito.
Da farko mahaifin Waziran ya shaidawa jami'an 'yan sanda cewa ta mutu ne sakamakon wani hatsari da ya ritsa da ita.
Ya bayyana hakan ne bayan an tsinci gawarta kaca - kaca da jini da raunuka a kanta a gefen wani titi.
Amma daga baya ya janye jawabinsa tare da yin ikirarin cewa mijinta, Allah Baksh, da dan uwansa, Kareem Baksh, ne su ka kasheta.
Tuni rundunar 'yan sanda ta kama mijin da dan uwansa tare da tsaresu a caji ofis.
Wani lauya mai rajin kare hakkin bil'adama a kasar Pakistan, Ayaz Latif Palijo, ya wallafa faifan bidiyon mahaifin Waziran yayin da ya ke sharbar kuka a kan kabarinta.
A rubutun da ya wallafa tare da faifan bidiyon, lauya Palijo ya ce; "mahaifin matar da aka kashe kenan yayin da ya ke kuka a kabarinta, ya na neman a yi mata adalci.
"An kashe Waziran kwanaki hudu da su ka gabata ta hanyar jefeta a Dist Jamshoro da ke Sindh, amma har yanzu ba a kama wadanda suka aikata laifin ba.
DUBA WANNAN: 'Duk cikin ikon Allah ne': Shugaban 'yan fashi ya koma wa'azi a hannun SARS
"Har yanzu mazauna kauyuka da karkara a Pakistan su na amfani da al'adu wajen cigaba da kashe mata."
A irin wannan kisa na girmamawa ne wani miji a kasar Iran ya datse kan matarsa mai shekaru 19 bayan ta gudu daga gidansa kwanaki kadan bayan daura mu su aure.
Mijin, mai shekaru 23, ya aikata hakan ne a lokacin da ya hadu da matar bayan ya shafe shekara guda ya na nemanta.
Kungiyoyi da dama su na korafi a kan irin wannan al'ada tare da yin kira ga hukumomi a kan su dauki matakan da su ka dace domin kare mata daga irin kisa da ake yi wa lakada da 'kisan girmamawa'.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng