Bude makarantu: Afenifere ta na so a sallami Adamu Adamu da Hon. Nwajiuba

Bude makarantu: Afenifere ta na so a sallami Adamu Adamu da Hon. Nwajiuba

Kungiyar da ke da rajin kare zamantakewa da siyasar Yarbawa a Najeriya, Afenifere ta soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cewa ka da a bude makarantu.

Gwamnatin tarayya ta bakin ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu, ta ce babu dalilin da zai sa ta bude makarantu a halin yanzu da ake fama da annobar COVID-19.

Wannan mataki da gwamnati ta dauka na cigaba da rufe wuraren karatu yayin da ake daf da fara jarrabawar WAEC ta zuwa makarantun gaba da sakandare bai yi wa wasu dadi ba.

Kungiyar Afenifere ta na cikin wadanda su ka soki wannan lamari, su ka kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige duka Ministocinsa na ilmi.

Ministan ilmi na kasa shi ne Malam Adamu Adamu, yayin da Hon. Chukwuemeka Nwajiuba ya ke rike da kujerar karamin minista na harkar ilmi a Najeriya.

Sakataren kungiyar Afenifere na kasa, Bashorun Sehinde Arogbofa ya zargi Ministan ilmi da kokarin zaunar da yaran makaranta na tsawon shekara guda ba su zuwa aji.

KU KARANTA: Minista ya fadi abubuwan da aka duba kafin a janye tallafin man fetur

Bude makarantu: Afenifere ta na so a sallami Adamu Adamu da Hon. Nwajiuba
Babban Ministan ilmi Adamu Adamu
Asali: UGC

Bashorun Sehinde Arogbofa a madadin kungiyar ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta bude makarantu, sannan ta kawo matakai da za a bi wajen kare lafiyar ‘yan makaranta.

Ya ce: “Shi Adamu Adamu kamata ya yi a tsige shi, ba zai maida makarantunmu kamar mu na zamanin da can ba. Sun samu watanni kusan shida su tsara abin da za ayi wa yaran nan.”

Me gwamnati ta yi? Ya tambaya.

“Hakan ya na nufin su biyu (Adamu Adamu da karamin ministan ilmi) ba su san abin da su ke yi ba, su tafi. Ina ganin cewa a sallami Ministocin biyu.”

“Ta ya wani daga cikinsu zai fito ya ce za a rubuta jarrabawa a watan Agusta, sai kuma wani ya fito ya warware abin da takwaransa ya fada?” inji kungiyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel