Lauyan Magu zai nemi a saki tsohon Shugaban hukumar EFCC a yau Juma’a

Lauyan Magu zai nemi a saki tsohon Shugaban hukumar EFCC a yau Juma’a

A yau Juma’a, 10 ga watan Yuli, 2020, lauyan da ke kare Ibrahim Magu, ya ce zai gabatar da takarda gaban ‘yan sanda ya na neman a saki tsohon shugaban hukumar EFCC.

Barista Oluwatosin Ojaomo ya fadawa jaridar Punch cewa ya na shirin karbo belin Ibrahim Magu daga hannun jami’an tsaro.

Oluwatosin Ojaomo ya bayyana cewa bai iya samun damar haduwa da Ibrahim Magu a ranar Alhamis ba, duk da cewa ya dauki tsawon lokaci a ofishin ‘yan sanda ya na jiran tsammani.

A jiya Lauyan ya bata lokaci har zuwa cikin dare a sashen binciken laifuffuka na CID da ke ofishin ‘yan sanda a unguwar Garki, babban birnin tarayya Abuja.

Lauyan ya shaidawa ‘yan jarida cewa: “Yanzu na ke barin FCID bayan na bata lokaci domin in sadu da Magu, amma ba su fito da shi daga fadar shugaban kasa ba.”

Ojaomo ya bayyana haka ne da kimanin karfe 8:30 na dare.

A cewarsa, gobe (Yau kenan yanzu) zai nemi jami’an ‘yan sanda su saki Magu a kan beli. Ya ce: “Gobe zan rubuta takarda in gabatar a gaban ‘yan sanda domin a sake shi.”

KU KARANTA: Magu: Osinbajo da 'Dan jarida za su fafata a kotu

Lauyan Magu zai nemi a saki tsohon Shugaban hukumar EFCC a yau Juma’a
Ibarahim Magu
Asali: UGC

A wata hirar dabam, lauyan ya bayyana cewa: “Mu na cigaba da kokarin ganin mun karbo belinsa. Ina wurin da sassafe, amma aka fada mani an wuce da shi zuwa fadar shugaban kasa.”

Lauyan na sa ya kara da cewa: “Ba su nuna mana wata takarda da ta bada damar tsare shi ba. Amma an fada mani cewa ba a muzguna masa.”

Ya ce: “Matsalar ita ce muddin aka dauke shi daga FCID tun kusan karfe 8:00 na safe, ya na kasancewa a fadar shugaban kasa har yamma.”

”DIG ne kawai ya isa ya bada belinsa domin shi ya ke tsare da shi. Kuma ina kokarin in hadu da shi a game da lamarin.” Inji Lauyan.

A game da halin da tsohon shugaban na EFCC ya ke ciki, Ojaomo ya ce a karshe Magu zai yi nasara, kuma babu dalilin a cigaba da tsare shi ba tare da iznin hukuma ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel