'Nagode Allah da 'yan sanda su ka kama mu' - Shugaban 'yan fashi
A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sanda ta yi holin wata tawagar 'yan fashi da makami da su ka kashe jami'an 'yan sanda 6 a tsakanin shekarar 2019 zuwa farkon shekarar 2020 yayin da su ka je fashi wasu bankuna guda uku a jihar Ekiti da Ondo.
Shugaban tawagar 'yan fashin guda bakwai, Tajo Tubonsun, mai shekaru 42, ya ce ya godewa Allah da 'yan sanda su ka kamasu.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa laifin aikata fashi da makami a hedikwatar rundunar 'yan sandan SARS da ke Abuja.
Tubonson ya jagoranci tawagarsa zuwa wajen aikata fashi da makami a bankuna guda uku a tsakanin shekarar 2019 da farkon shekarar 2020.
"A tsakanin shekarar 2019 da wani bangare na wannan shekarar, wannan tawaga ta aikata fashi a wasu bankuna guda uku da ke; Ile-Oluji da Idanre a jihar Ondo da kuma Oye a jihar Ekiti.
"Sun kai harin ne a lokuta daban - daban tare da kashe jami'an 'yan sandan da suka samu a bankunan," a cewar Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya.
Da ya ke karin bayani a kansu, Mba ya bayyana cewa 'yan fashin guda 7 su na aiki bisa tsarin kwarewar kwararrun 'yan ta'adda.
Ya kara da cewa; "daga cikin tawagar akwai mutane biyu da ke sana'ar achaba, aikinsu kawai shine su ke lura da motsin mutane da kuma zuwan jami'an tsaro domin sanar da sauran tawagar da ke yin fashi a banki."
Da ya ke magana amadadin sauran 'yan tawagarsa, Tubonson ya bayyana cewa ya godewa Allah da 'yan sanda su ka kamasu saboda komai ba ya faruwa sai da yardarsa, a saboda haka batun kamasu ma ikon Allah ne.
"Akwai manufar Allah a kanmu, shine kadai kuma ya santa. Mun gode Allah da 'yan sanda su ka kama mu domin tare da ikonsa ne aka samu nasarar kamomu.
DUBA WANNAN: 'Yan arewa sun shawarci Buhari a kan mutumin da ya dace ya maye gurbin Magu idan ana son ganin aiki da cikawa
"Mun san mu ma su zunubi ne, mun yi wa Allah laifi. Mun riga mun roki Allah, ni da kaina na roke shi, ya yafe mana. Yanzu kuma ina rokon jama'a su yafe mana, Allah zai taimakemu da albarkacin Yesu," a cewar Tubonson.
Tubonson, wanda ya bayyana cewa ya fara fashi da makami a shekarar 2018, ya kara da cewa su na amfani da manyan bindigu na gida da na ketare irinsu AK47 da sauransu.
Dangane da kisan jami'an rundunar 'yan sanda, Tubonson ya bayyana cewa babu hannunsa kuma babu izininsa, inda ya bayyana cewa yaransa ne da ke tsayawa a harabar banki yayin fashi su ka harbe 'yan sandan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng