Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu?

Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu?

- Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie, ta yi martani a kan rahoton da ke yawo mai cewa an maye gurbin dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu

- Kamar yadda Onochie ta bayyana, ta ce bata ji dadin rahotannin da ke yawo ba mai sanar da cewa an maye gurbin dakataccen shugaban EFCC

- Hadimar shugaban kasar ta yi kira ga jama'a da su dinga jira har sai takarda ko jawabi ya fito daga jami'an gwamnati kafin su fara yada komai

Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ba a maye gurbin Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa ba.

Onochie ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a wallafar da tayi ta ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, domin martani a kan labaran da ke yaduwa na cewa an maye gurbin Magu.

Hadimar shugaban kasa ta bayyana rashin jin dadin ta yadda ake yada cewa an maye gurbin Magu da mutane daban-daban har biyar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli don shugabantar EFCC bayan dakatar da Magu.

Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu?
Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A yayin jajanta yadda jama'a ke fadawa tarkon labaran bogi, ta yi kira ga jama'a da su dakata har sai an fitar da sanarwa a hukumance.

Onochie ta kara da cewa, babu girma a yada labaran bogi.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu

Ta ce: "Mutane mabanbanta har 5 aka nada jiya domin su shugabanci EFCC. Abun bakin ciki ne yadda muka zama hedkwatar labaran karya a yanzu.

"Hatta da shafukan sadarwa na al’ada sun fada tarkon a baya bayan nan, an nada mutane da dama a matsayin Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa. Illa mai girma Gambari, wanda ya samu matsayin. Bamu koyi darasi ba."

Ta kara da cewa: "Abinda kowa ya kamata yayi shine dakatawa. Mu jira har sai an fidda sanarwa daga hukuma. Son fara sanar da labarai na daga cikin abinda ke kai jama'a yada labaran bogi."

"Babu martaba a buga labarin karya da dumi-duminta. Mu yi hakuri har sai mun ji daga majiyoyi na hukuma."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng