Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu

Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu

A ranar Laraba, dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, ya sake fuskantar kwamitin bincike a rana ta uku a kan zargin da Antoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami ke masa.

Ya amsa tambayoyi na sama da sa'o'i 10 inda daga nan aka mayar da shi sashen bincike na musamman inda aka tsaresa, jaridar The Nation ta ruwaito..

Kwamitin ya sake fadada bincikensa ta hanyar gayyatar manyan jami'an EFCC da kuma sashen binciken sirri na kudi na Najeriya (NFIU) don su amsa tambayoyin su.

Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu
Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu Hoto: The Cable
Asali: UGC

Wasu daga cikin zargin da ake masa sun hada da:

1. Zargin banbanci a bayanin sassanci tsakanin EFCC da ma'aikatar kudi a kan kudaden da aka samo wanda 'yan siyasa suka wawura.

2. Bayyana cewa an samo N539 biliyan a maimakon N504 biliyan da ya fara ikirarin an samo.

3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni janar din tarayya ta hanyar yanke hukuncin ba tare da tuntubarsa ba.

4. Rashin bada bayanai gamsassu a kan tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Mudueke.

5. Zarginsa da ake da rashin daukar matakin da ya dace kuma a kan lokaci a kan binciken Process and Industrial Development (P&ID) wanda hakan ya kawo rikici.

6. Rashin mutunta umarnin kotu na sakin asusun bankin tsohon shugaban First Bank wanda ke dauke da N7 biliyan.

7. Tsaiko wajen yanke hukuncin a kan wasu gangunan man fetur biyu da sojin ruwa suka kwace wanda hakan ya janyo asarar danyen man fetur.

8. Zargin bai wa yaransa masu bincike fifiko, wadanda ake kira da 'Magu boys'.

9. Kai karar wasu alkalai zuwa ga shugabanninsu ba tare da tuntubar AGF ba.

10. Zargin siyar da kayan da aka kwace ga masoya, makusanta da abokai.

Wannan kwamiti da Mai shari'a Ayo Salami ke jagoranta na zama ne a fadar shugaban kasa. An gayyato sakataren EFCC Ola Oluyede da daraktan ayyuka, Mohammed Umar.

Sauran sun hada da daraktan bangaren kudi, daraktan al'amuran cikin gida da wasu jigo a NFIU.

An gano cewa, shugaban kwamitin, Mai shari'a Salami, wanda shine tsohon shugaban kotun daukaka kara, ya tabbatar wa da Magu tare da sauran cewa za a yi musu adalci.

Hakazalika, kwamitin ya tabbatar da cewa bai san labarin dakatar da Magu ba daga ofishinsa.

An gano cewa, Magu ya yi alkawarin bada duk takardu ko fayel da ake bukata don bincike. Ya kara sanar da kwamitin cewa bai taba kin biyayya ga ministan shari'ar ba.

KU KARANTA KUMA: Daukan ma’aikata 774,000: Adadin gurbin da za a bai wa Gwamnoni, 'yan majalisu da ministoci

Ya kara da cewa, bai taba barazana ga wani alkali ba, ballantana mai shari'a Binta Murtala-Nyako, wacce AGF ya ce a takardar sa.

Kamar yadda daya daga cikin majiyoyi ta tabbatar, shugaban EFCC ne yace a gayyaci dukkan shugabannin cibiyoyin da suka dace don su yi martani a kan zargin da da ake.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel