Zaben Gwamnan Ondo: APC ta tantance Akeredolu da manema takara biyar
A yayin da jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fidda gwanin takara a ranar 20 ga watan Yuli, a jiya Laraba ne aka tantance gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamnan na daya daga cikin 'yan jam'iyyar APC 12 da ke hankoron samun tikitin tsayawa takara a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba na 2020.
Sauran wadanda jam'iyyar ta tantance kawo yanzu sun hadar da; Ambasada Olusola Iji, Cif Odimayo Okunjimi, Cif Olayide Adelaml, Cif Isaac Kekemeke da kuma Cif Olusola Oke.
Jerin manema takara da jam'iyyar za ta tantance a yau Alhamis sun hadar da; lfeoluwa Oyedele, Olajumoke Anifowoshe, Awodeyi Akinsehinwa, Akinola Colinus, Olubukola Olarogba, Okunola Adetula, Dr. Segun Abraham da Dr. Nathaniel Adojutelegan
A wani sako da gwamnan jihar mai ci ya wallafa kan shafinsa na Facebook, ya yabawa mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar dangane da tsarin tantancewar da suka tanada.
Ya rubuta cewa: "Yanzu haka dai jam’iyyata ta @OfficialAPCNg ta kammala tantance ni.
"Mambobin kwamitin sun kasance su na dubawa sosai, sun binciki duk wasu takardu tare da gabatar da tambayoyi. Na yi imanin cewa jam'iyyar ta tanadi tsari mai kyau."
A ranar da ta gabata ne dai kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa, ya amince da tsarin amfani da wakilai a madadin 'yar tinke wajen fidda gwanin takarar gwamnan jihar.
Wannan babban jami'i na jam'iyyar, shi ne ya bayar da tabbaci kan tsarin fidda gwanin takara da jam'iyyar ta rike kuma har an sanar da hakan ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC.
Sai dai mutum 11 daga cikin manema tikitin takarar gwamna na jam'iyyar, sun yi kira da a yi amfani da tsarin 'yar tinke wato kato bayan kato a yayin zaben fidda gwanin takarar.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a Larabar da ta gabata ne wasu mutane suka hau kan tituna a babban birnin tarayya Abuja, su na zanga-zanga a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
KARANTA KUMA: Tsofaffin gwamnoni 4 da Magu ya sa aka tura gidan yari
Masu zanga-zangar su na kira ga gwamnati ta kama babban jagoran na jam’iyyar APC wanda ya fito daga shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.
An taso fitaccen ‘dan siyasar a gaba ne a dalilin wasu manyan motocin daukar kudi har biyu da aka gani sun shiga gidansa da rana tsaka a shekarar da ta wuce.
Wannan abu ya faru ne a lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya.
Tsohon gwamnan na Legas bai karyata wannan lamari ba a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida a cikin watan Fabrairun 2019.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng