Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651

Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651

A ci gaban tabbatar da kawo zaman lafiya da dakarun sojin Najeriya ke yi, rundunar Operation Hadarin Daji karkashin Operation Accord a ranar 7 ga watan Yulin 2020, ta hadu da 'yan bindiga a karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.

A yayin amfani da salon iya yaki, dakarun sunyi musayar wuta da 'yan bindigar, inda suka kashe biyu daga ciki. Wasu daga ciki sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.

Hakazalika, a ranar 8 ga watan Yuli 2020, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri a kan kaiwa da kawowar 'yan bindigogi masu tarin yawa. Sun tsaresu a yayin da suke tafiya da shanun sata zuwa kauyen Jangemi da ke kusa da garin Kwaren Ganuwa.

Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651
Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

Tuni dakarun suka tsare 'yan bindigar a kauyen Bawaganga. Bayan ganin dakarun da suka yi, sun tsere inda suka shiga dajin Muhaye tare da barin shanu 250 da raguna 150. A halin yanzu ana tsare da dabbobin.

A wani ci gaba da ya faru a ranar 8 ga watan Yulin 2020, dakarun sun kai samame wurin Kwaren Ganuwa da ke kusa da Tsafe inda suka samo dabbobi masu tarin yawa. 'Yan bindigar sun tsere bayan ganin dakarun.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin, John Eneche ya fitar a wata takarda, ya ce a ranar dakarun sun samo shanu 117 da tumaki 34.

Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651
Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohon shugaban hukumar DSS ya bai wa Magu shawara

Hakazalika, a wani sintiri da dakarun suka yi na ranar 7 ga watan Yuli, sun kama wani Ibrahim Alhassan. Bayan bincikarsa da aka yi, an gano cewa dan kungiyar 'yan bindigar Kachalle ne.

Wanda ake zargin, ya amsa cewa ana bashi N150,000 a duk lokacin da suka da suka yi aika-aikarsu. A halin yanzu yana tsare kuma ana ci gaba da bincike.

Dakarun sun damke wasu 'yan bindiga 3 a kan titin unguwar Doka zuwa Sabon layi na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina. Sun kashe daya yayin da sauran suka sha da kyar da raunikan harbin bindiga.

Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651
Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

A wannan halin an samu bindiga daya kirar AK 47 da babur daya.

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Daji a kan jajircewarsu da kwarewarsu.

Ya kara kira ga dakarun da su tsananta ayyukansu ta hanyar hana 'yan ta'adda sakat a fadin kasar nan har sai zaman lafiya ya dawo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel