Yadda aka shigo da tsarin albashin CONLESS ya sabawa ka’ida – Inji Yemi-Esan

Yadda aka shigo da tsarin albashin CONLESS ya sabawa ka’ida – Inji Yemi-Esan

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan, ta ce akwai matsala a game da tsarin albashin CONLESS na ma’aikatan gwamnati da ke majalisa tarayya.

Misis Folasade Yemi-Esan ta bayyana cewa yadda ake aiki da tsarin CONLESS ya sabawa doka.

Jaridar The Cable ta fahimci cewa shugaban ma’aikatan gwamnatin ta yi wannan jawabi ne a lokacin da ta gana da shugabannin majalisar tarayya a garin Abuja.

Folasade Yemi-Esan ta zauna da shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da kuma takwaransa na majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.

Rahoton da mu ka samu ya ce Yemi-Esan ta bukaci Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila su maida albashin ma’aikatan da ke majalisa a kan tsarin da su ke kai da can a baya.

A ‘yan shekarun baya an samu wasu ma’aikatan gwamnati da ke aiki da majalisa wanda su ka rika kukan cewa ba su san albashi mai tsoka, wannan ya sa aka kara masu kudi.

KU KARANTA: Abin da Pantami ya ke samu a jami'a, ya fi albashin Minista

Yadda aka shigo da tsarin albashin CONLESS ya sabawa ka’ida – Inji Yemi-Esan
Shugabannin Majalisar Tarayya
Asali: UGC

Bukola Saraki ne ya jagoranci wannan canji da aka samu a albashin ma’aikatan gwamnatin a lokacin da ya ke rike da kujerar shugaban majalisar dattawa a Najeriya.

A yanzu kuma shugaban ma’aikatan gwamnati ta kasa ta fadawa 'yan majalisar cewa akwai wasu kura-kurai da aka samu wajen dabbaka wannan sabon tsarin albashi.

A cewar Folasade Yemi-Esan, ma’aikatan gwamnati da ke aiki a majalisa ba su da bambanci da sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke wasu ma’aikatu a fadin kasar nan.

Bayan cewa ma’aikatan ba su bukatar a ba su wani albashi na dabam, Yemi-Esan ta ce akwai matakai da ake bi a ka’idar gwamnati kafin a kawo sabon tsarin albashi.

Akwai ma’aikatan gwamnati na musamman wadanda su ke aiki da bangaren ‘yan majalisa. Sai da ta kai wdanan ma’aikata sun yi zanga-zanga domin ganin sun samu kari a albashinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng