Sunaye: Bagudu ya amince da nadin sabbin hakimai 5 a jihar Kebbi

Sunaye: Bagudu ya amince da nadin sabbin hakimai 5 a jihar Kebbi

- Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da nadin wasu sabbin hakimai biyar da kuma shugaban masarauta

- Gwamna Atiku Bagudu ne ya bayar da wannan umurni

- Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da kwamishinan kananan hukumomi da al'amuran masarautu, Hasdan Muhammad Shalla ya fitar

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da nadin sabbin hakimai biyar da kuma shugaban masarauta.

A wata takarda da kwamishinan kananan hukumomi da al'amuran masarautu, Hasdan Muhammad Shalla ya fitar, ya bayyana wadanda za a yi wa nadin.

Sun hada da: Hasdan Sulaiman Jiga a matsayin hakimin Dangamaji a karamar hukumad Jega, Umaru Mohammed Dodo Aliero a matsayin hakimin Sabiyel da ke karamar hukumar Aliero.

Sunaye: Bagudu ya amince da nadin sabbin hakimai 5 a jihar Kebbi
Sunaye: Bagudu ya amince da nadin sabbin hakimai 5 a jihar Kebbi Hoto: Nigerian Observer
Asali: Twitter

Haka zalika za a nada Dr. Abubakar A. Koko a matsayin hakimin Lani da karamar hukumar Koko Besse.

Sauran sun hada da; Aliyu D. Zagga a matsayin hakimin Kende da ke karamar hukumar Bagudo, Bashar Aliyu Muzan Kimba a matsayin hakimin Kiba da ke karamar hukumar Jega.

KU KARANTA KUMA: Korona: Rabon da na ga shugaban ma’aikatana tun watanni biyu kafin mutuwarsa - Gwamnan Kwara

Alhaji Kabiru Abdullahi a matsayin Kokanin Kabi, shugaba a masarautar Argungun da ke karamar hukumar Argungun.

A wani labari na daban, majalisar dattawa a ranar Laraba, ta karbi wata bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari na maye gurbi tare da tabbatar da wasu jakadu biyu.

Bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya karanto a zauren majalisar.

Shugaban kasar ya bukaci a maye nadin Mista Oboro Effiong Akpabio da na Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar wanda aka yi da farko.

Wasikar ya zo kamar haka: “daidai da sashi na 171(1)(2)(c) da karamin sashe na (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya kamar yadda aka gyara, Ina mika sunayen Mista John J. Usanga da Air Commodore Peter Anda Bakiya Gana (mai ritaya) daga jihohin Akwa Ibom da Niger domin a tabbatar da su, a matsayin jakadu.

“Ina bukatar majalisar dattawa da ta yi kiranye ga sunayen da na fara gabatarwa na Mista Oboro Effiong Akpabio da Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar daga Akwa Ibom da Borno.

“Wasikar mai kwanan wata 17 ga watan Yuni 2020, na canza sunan Mista Oboro Effiong Akpabio da na Mista John J. Usanga (jihar Akwa Ibom). Na maye gurbin Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar (jihar Borno) da Air Commodore Peter Anda Bakiya Gana (jihar Niger).”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel