Kwallon kafa: Cutar COVID-19 ta harbi ‘Dan wasan Genk Paul Onuachu

Kwallon kafa: Cutar COVID-19 ta harbi ‘Dan wasan Genk Paul Onuachu

- Paul Onuachu mai bugawa kungiyar Genk ya kamu da cutar Coronavirus

- Genk ta bada umarnin cewa ‘Dan wasan gaban ya yi maza ya killace kansa

- Onuachu ya na cikin wadanda su ka bugawa Najeriya a gasar AFCON 2019

A ranar 8 ga watan Yuli, 2020, aka tabbatar da cewa ‘dan wasan gaban Super Eagles, Paul Onuachu, ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.

Sakamakon gwajin da ya fito a jiya ranar Laraba ya nuna cewa babu shakka ‘dan wasa Paul Onuachu mai shekara 26 ya kamu da wannan cuta a kasar Beljika.

Gwajin da aka yi ya nuna cewa sauran takwarorinsa ‘Yan Najeriya da ke bugawa kungiyar Genk Stephen Odey da Cyril Dessers ba su dauki cutar ba.

Jaridar Punch ta ce Paul Onuachu shi ne ‘dan kwallon Super Eagles na biyu da aka sani mai dauke da COVID-19. A watan Fubrairu, Akpan Udoh ya kamu da cutar.

KU KARANTA: Yadda wasu Taurarin Barcelona su ka kamu da COVID-19

Kwallon kafa: Cutar COVID-19 ta harbi ‘Dan wasan Genk Paul Onuachu
'Dan wasa Paul Onuachu
Asali: Getty Images

Ga jawabin da kulob din ta fitar a shafinta na yanar gizo a ranar Laraba:

“A lokacin da ake shiryawa wasan farko na kakar bana, an yi wa daukacin ‘yan kungiyar Genk gwajin COVID-19 a jiya (Talata).”

“An samu cewa babu mai dauke da kwayar cutar face Paul Onuachu.”

Dogon ‘dan wasan ya dawo Najeriya ne a watan Mayu tare da Victor Osimhen and Imoh Ezekiel. A karshen watan Yuni ya iya komawa kasar da ya ke wasa.

Kamar yadda mu ka samu labari ‘dan kwallon ya makale a Legas na kusan mako guda a sakamakon takunkumin da gwamnatin Najeriya ta sa na hana jirage sauka da tashi.

A shekarar da ta wuce ne Onuachu ya koma bugawa kungiyar Genk bayan ya bar Midtjylland. Kafin a dakatar da wasanni saboda annobar, ‘dan wasan ya zura kwallaye 10.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel