Dokar haramta lalata da ‘Yan mata a manyan makarantu ya samu shiga a Majalisa

Dokar haramta lalata da ‘Yan mata a manyan makarantu ya samu shiga a Majalisa

A ranar Talata, 8 ga watan Yuli, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin da za ta haramtawa malaman manyan makarantu yi wa ‘dalibai barazana.

Ana kukan cewa ‘daliban makarantu gaba da sakandare kamar jami’o’i da kwalejin ilmi su na fuskantar kalubale, musamman ‘yan mata.

Wannan kudiri mai suna: “The Sexual Harassment Bill, 2020” zai cire uzurin da malaman makarantu su ke amfani da shi wajen lalata da ‘dalibansu.

Jaridar Daily Trust ta ce Malamai su kan fake da cewa yara sun yarda kafin su tara da su, don haka wannan kudiri da aka kawo zai yi garambawul ga wasu dokoki masu ci.

Kungiyar malaman jami’a watau ASUU ba ta goyon bayan wannan kudiri. A watan Fubrairu, shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce tun can akwai irin wannan doka a kasa.

KU KARANTA: An gano wani ‘Dan shekara 50 da ya ke lalata da Mai shekara 8

Dokar haramta lalata da ‘Yan mata a manyan makarantu ya samu shiga a Majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta amince da wannan kudiri ya zama dokar kasa ne bayan shugabar kwamitin harkar shari’a da kare hakkin mutane, Sanata Opeyemi Bamidele ya nuna na’am dinsa.

Sanatan na Ekiti ta bayyana cewa rashin dokoki sun taimaka wajen jawo yadda matsalar fyade da barazanar lalata da ‘yan makaranta ta yi kamari a Najeriya.

Opeyemi Bamidele a rahoton da ya gabatar a zauren majalisar tarayya, ya ce wannan barazana ya na cikin abin da ke jawo matsala wajen tabarbarewar karatun boko a kasar nan.

Barazanar lalata da yaran makaranta ya sababba lalacewar harkar ilmi, wanda wannan ya jawo ake samun ruba-ruba sun kammaka karatu, tare da kawo rashin tarbiyya da sanin aiki a makarantu.

A jawabinsa, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce su na son ganin dalibai sun samu damar daukar karatu a makarantu ba tare da fama da wani kalubale ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel