Korona: Rabon da na ga shugaban ma’aikatana tun watanni biyu kafin mutuwarsa - Gwamnan Kwara
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya ce rabon da ya yi ido hudu da shugaban ma’aikatansa, Adisa Logun, ya kasance tun a ranar 6 ga watan Afrilu.
Watanni biyu kenan kafin mutuwarsa a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, sakamakon cutar coronavirus.
Mista Abdulrazaq ya bayyana hakan ne a wani jawabi ta hannun kakakinsa, Olayinka Fafoluyi a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.
Mista Fafoluyi ya ce gwamnan ya yi haduwar karshe da Mista Logun a lokacin kaddamar da shirin rabawa tsoffi kudi na hannu da hannu.
Ya ce duk tarukan da suka biyo baya tsakanin gwamnan da shugaban ma’aikatansa an yi su ne ta yanar gizo, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jawabin ya ce jami’an gwamnati da suka hadu da Mista Logun a baya-bayan nan duk sun killace kansu.
“Jami’an jihar Kwara wadanda suka hadu da marigayi shugaban ma’aikatan Gwamnatin jihar, Aminu Adisa Logun a makonni biyu da suka gabata duk sun shiga killace kai yayinda aka dauki samfurinsu don gwajin korona," cewar jawabin.
KU KARANTA KUMA: Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi
Mista Logun ya rasu a ranar Talata, yan sa’o’i kadan bayan sakamakon gwajinsa ya nuna yana dauke da korona.
Gwamnatin jihar ya kaddamar da hutun kwanaki bakwai don karrama shi.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Allah ya yi wa shugaban ma’aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa Logun, rasuwa.
Babban hadimi na musamman ga gwamnan jihar Kwana kan harkokin labarai, Fafoluyi Olayinka ne ya tabbatar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter.
Ya rasu yana da shekaru 73 a duniya, jaridar The Nation ta ruwaito.
Ya ce: “Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kwara, Aminu Adisa Logun, ya rasu. Shakka babu mutuwa itace abu na gaba bayan haihuwa. Bakar Talata ta zo a Kwara.”
KU KARANTA KUMA: Manyan jami’an yan sanda sun fara kamun kafa domin maye gurbin Ibrahim Magu a EFCC
An nada marigayi Aminu Adisa Logun a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kwara a 2019, yan makonni kadan bayan rantsar da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng