Zaben 2015: An bukaci INEC ta mayar da rarar N73bn da ta karba

Zaben 2015: An bukaci INEC ta mayar da rarar N73bn da ta karba

Kwamitin majalisar wakilai ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta mayar da rarar biliyan N73 da ake zargin ta karba lokacin zaben shekarar 2015.

Kwamitin, mai kula da yadda ake kashe kudaden jama'a, ya yi zargin cewa INEC ta karbi rarar biliyan N73 daga ofishin babban akanta na kasa (AGF) bayan biliyan N45 da aka fara bawa hukumar domin gudanar da zaben 2015.

Shugaban kwamitin, Wole Oke, da sauran mambobinsa sun kafe a kan cewa sai hukumar INEC ta mayar da rarar kudaden asusun gwamnati.

Kwamitin ya zargi ofsishinAGF da karya ka'ida wajen kasafta kudaden gwamnati sabanin ikon da ya ke da shi.

'Yan majalisar sun bukaci ofishin AGF ya mayar da rarar wata biliyan N16.9 daga cikin biliyan N36.9 da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a bawa INEC amma sai iya biliyan N10 ofsihin AGF ya bawa hukumar.

A cewar shugaban kwamitin, warewa INEC biliyan N107.7 da kuma kara mata wata biliyan N73 sabanin biliyan N45 da aka fara amincewa da bawa hukumar daidai ya ke da sabawa doka, wanda bai kamata ofishin AGF a aikata hakan ba.

Zaben 2015: An bukaci INEC ta mayar da rarar N73bn da ta karba
Shugaban INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Original

Batun neman INEC ta mayar da biliyan N73 na zuwa ne a daidai lokacin da wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa ke binciken Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da cin hanci.

Magu, wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da shi, ya na fuskantar tuhume - tuhume ma su nasaba da almundahana da kama karya a gudanar da aikinsa na yaki da cin hanci.

A ranar Litinin ne Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin bincikensa da aka kafa a fadar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Magu ya saduda, ya dauki babban lauyan da zai wakilce shi a gaban kwamitin bincike

Bayan ya bar gaban kwamitin a ranar Litinin, jami'an rundunar 'yan sanda sun yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu, inda aka tsare shi har zuwa ranar Talata.

Yanzu haka Magu ya dauko hayar babban lauya, Kanu Agabi (SAN), domin ya wakilce shi a gaban kwamitin bincike.

Kafin ya dauko hayar Agabi, lauyan Magu, Oluwatoyin Ojaomo, ya ce masu son ganin maigidansa sun fi annobar korona karfi.

Ojaomo ya bayyana hakan ne a cikin shirin gidan talabijin na Channels yayin da ya ke mayar da martani a kan gayyatar da wani kwamitin shugaban kasa ya yi wa Magu a ranar Litinin.

Lauyan ya ce kwamitin bincike ya gayyaci Magu ne domin ya yi bayani a kan gibin da aka samu a adadin kudin da EFCC ta saka a aljihun gwamnati da kuma wanda Magu ya sanar a bainar jama'a.

A cewar Lauyan, adadin kudin da Magu ya mayar aljihun gwamnati sun zarce adadin kudin da ya sanar EFCC ta kwace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel